Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Kirsimeti: Gwamnan Gombe Ya Biya Albashin Disamba Ranar 20

Daga Idris Khalid Gwamnan Jihar Gombe Muhammadu Inuwa Yahaya ya umarci ma’aikatar kudi ta jihar ta biya albashin watan Disamba g...


Daga Idris Khalid

Gwamnan Jihar Gombe Muhammadu Inuwa Yahaya ya umarci ma’aikatar kudi ta jihar ta biya albashin watan Disamba ga ma’aikata tun daga ranar Litinin 20 ga wannan wata.

Gwamnan ya dauki wannan matakin ne domin saukaka wa ma'aikata da al'ummar jihar dawainiyar gudanar da bukukuwan Kirsimeti da na sabuwar shekara cikin annashuwa da farin ciki.

A wata sanarwar da kakakin gwamnan Malam Isma'ila Uba Misilli ya fitar, ya bayyana cewar bisa al'ada gwamnatin jihar na fara biyan albashin ma'aikatan jihar daga ranar 25 zuwa 26 na kowace wata, amma sakamakon bukukuwan Kirsimeti da na sabuwar shekara ya bada umarci biya domin faranta ran wadanda lamarin ya shafa. 

"Hakazalika Gwamna Inuwa ya ce gwamnatinsa za ta cika alkawarin biyan tsofin ma'aikatan da suka yi ritaya naira biliyan 1 da miliyan 500 a jihar a matsayin giratutin da suke bi tun zamanin gwamnatin da ta shude."

No comments