Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Kirsimeti: Gwamnan Gombe Ya Saki Naira Miliyan 25 Da Kayayyakin Abinci Ga Al'ummar Kiristocin Jihar

Daga Idris Khalid A ci gaba da shirye-shiryen bukukuwan Kirsimeti da na sabuwar shekara, Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Ya...


Daga Idris Khalid

A ci gaba da shirye-shiryen bukukuwan Kirsimeti da na sabuwar shekara, Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya ya bayar da tallafin naira miliyan 25 ga mabiya addinin Kirista a jihar.

A sanarwar da Ismaila Uba Misilli, Babban Daraktan Yada Labarun Gwamnan Jihar Gombe ya fitar na cewa, wannan matakin wani bangare ne na karimcin da Gwamna Inuwa yake yiwa Kiristocin Jihar Gombe don basu damar gudanar da bikin karshen shekara cikin walwala duba da halin matsin tattalin arziki da ake ciki.

Baya ga naira miliyan 25, Gwamna Inuwa ya bayar da buhunan shinkafa dubu 2 da galan din man gyada 500 da katon na taliya Sphagetti 500 da buhunan Suga 200 da kuma kwalin Tumatir 200 ga mabiya addinin na Kirista.

Tun a ranar Litinin 20 ga wannan watan ne Gwamna Inuwa Yahaya ya amince da biyan albashin watan Disamba ga daukacin ma’aikatan gwamnati da masu rike da mukaman siyasa da na kananan hukumomi a Jihar Gombe don saukaka bukukuwan Kirsimeti cikin farin ciki ga 'yan uwa Kiristoci.

Ya ce, "Wannan karimcin da Gwamnan ya yi, ya dace da kudurinsa na inganta jin dadin al’ummar Jihar Gombe."

No comments