Jagoran 'yan adawar Kamaru Maurice Kamto tare da magoya bayansa. REUTERS/Zohra Bensemra RFI ta labarto cewa kotu a kasar Kamaru ta yan...
Jagoran 'yan adawar Kamaru Maurice Kamto tare da magoya bayansa. REUTERS/Zohra Bensemra |
RFI ta labarto cewa kotu a kasar Kamaru ta yanke hukuncin dauri kan magoya bayan madugun ‘yan adawar kasar Maurice Kamto su 47, ciki har da mai magana da yawunsa da kuma ma’ajin kudi na jam’iyyarsa, saboda samunsu da laifin yi wa kasar tawaye.
Hukunce-hunkuncen
dai sun kama ne daga daurin shekara 1 zuwa 7 a gidan Yari, kamar dai yadda wani
kusa a jam’iyyar adawa MRC ta Maurice Kamto ya sanar.
Su
dai wadannan mutane 47 da aka yanke wa hukuncin daurin, an kama su ne tun ranar
22 ga watan Satumban shekarar 2020, lokacin da jam’iyyarsu da wasu jam’iyyun
adawa suka shirya zanga-zangar adawa da shugaba Paul Biya wanda ke kan karagar
mulkin kasar ta Kamaru yau shekaru 39.
A
wancan lokaci, ‘yan sanda sun yi amfani da karfi domin tarwatsa tarzomar
musamman ma a birnin Douala, inda suka cafke sama da mutane 500, kuma yanzu
haka 124 daga cikinsu na tsare, a cewar jam’iyyar ta MRC.
Kakakin
babbar jam’iyyar adawar, Olivier Bibou Nissack da ma’ajin kudin jam’iyyar Alain
Fogue na daga cikin wadanda kotun sojin da ta yi zamanta a birnin Yaounde ta
daure.
No comments