Wata kotu a Birtaniya ta umurci Sarkin HaÉ—aÉ—É—iyar Dalar Larabawa Sheikh Mohammed bin Rashid al-Maktoum ya biya tsohuwar matarsa ...
Wata kotu a Birtaniya ta umurci Sarkin Haɗaɗɗiyar Dalar Larabawa Sheikh Mohammed bin Rashid al-Maktoum ya biya tsohuwar matarsa haƙƙin aure, da ya haura sama da dala miliyan 700, kwatankwacin kusan Naira biliyan 300.
Alƙalin babbar kotun ta Landan, ya ce Sarauniyar da ƴaƴanta na fuskantar gagarumar barazana daga mahaifinsu.
Alƙalin ya ce za ta iya amfani da kuɗaɗen wajen samar mata da tsaro, kama daga kan siyan motoci masu sulke da jami'ai na musamman da za su rika ba ta kariya da ƴaƴanta.
A shekarar 2019 ne Sarauniyar ta gudu zuwa Birtaniya saboda zargin neman rayuwarta da ta ce mahaifin Æ´aÆ´an na ta ke yi.
No comments