Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya roki masu kwatanta ayyukansa da na sauran gwamnoni da su daina. Ya yi rokon ne a wata sanarw...
Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara
Zulum, ya roki masu kwatanta ayyukansa da na sauran gwamnoni da su daina. Ya yi
rokon ne a wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Isa Gasau ya fitar a ranar
Litinin.
Gwamnan ya yaba wa mutanen da ke
tallata ayyukansa a shafukan sada zumunta, sai dai ya ce bai kamata a rika
kwatanta “ayyukana da na sauran gwamnoni ba, tun da dukkan jihohin suna da
bambanci”.
“Duk da yake Ina matukar godiya bisa
dukkan goyon baya da tallata ayyukana, a kwanakin nan, na samu sakonni, inda
ake kwatanta ayyukan da muke yi a Borno da na wasu jihohi, a wasu lokutan ma
ana zagi.
“Gaskiya ba na jin dadi a duk
lokacin da aka kwatanta ni da wani gwamna ta hanyar muzanta shi, musamman idan
wadanda suke yin hakan suna cikin masu amfani da shafukan sada zumuntar da ke
da alaka da mu”, in ji Gwamna Zulum.
No comments