Ku Dinga Yi Wa Gwamnatinmu Adalci – Buhari
Shugaban
Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana cewar kasar ta shiga matakin karshe na
yaki da kungiyar boko haram, yayin da ya sha alwashin murkushe su tare da yan
bindigar da suka hana zaman lafiya a yankin arewa maso yammacin kasar.
Buhari yace yana
sane da nasarorin da suke samu a matsayin gwamnati a arewa maso gabas da kuma
koma bayan da suke samu a arewa maso yamma, inda mutanen da suka fito daga wuri
guda da al’ada guda ke afkawa junan su suna sace dukiya da kuma kashe junan su.
Shugaban yace tuni ya bada odar sayo jiragen
saman yaki da manyan makamai daga Amurka tare da motocin yaki wadanda za’a
kaddamar da su akan irin wadannan mutane da suka hana zaman lafiya a Najeriya.
Buhari wanda ya baiwa sojoji umurnin afkawa
‘yan bindiga a jihohin Zamfara da Sokoto yace ba zasu ragawa wadannan mutanen
ba, saboda irin illar da suke yiwa jama’a.
Shugaban kasar ya bukaci ‘Yan Najeriya da su
yiwa gwamnatin sa adalci, lura da yadda suka samu kasar lokacin da suka karbi
mulki da kuma yadda take ayau.
Buhari yace mutanen arewa maso gabas sun fi
kowa sanin halin da ake ciki lokacin da ya karbi mulki, kuma sun bayyana haka
wajen irin tarbar da suka masa.
Shugaban yace da zaran wa’adin mulkin sa ya
kare zai sauka daga karagar mulki kamar yadda yayi alkawari lokacin da ya
rantse da Al Qur’ani cewar zai mutunta kundin tsarin mulki, saboda haka nan da
watanni 17 da ikon Allah zai sauka daga mulki domin baiwa wanda zai gaje shi
damar dorawa daga inda ya tsaya.
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
No comments