Hukumar tsaro ta farin kaya ta Najeriya DSS, ta gargaɗi ƴan ƙasar ciki har da sarakunan gargajiya da ƴan siyasa da malaman addin...
Lokutan bukukuwan ƙarshen shekara
Saƙon DSS ya ce kamar yadda aka sani ne bara-gurbi kan zafafa ayyukansu kafin lokuta da kuma bayan bukukuwan ƙarshen shekara.
Don haka ne ta yi kira ga shugabannin al'umma da masu otel-otel da masu kula da kasuwanni da tasoshi da wuraren shaƙatawa da su dinga taka tsantsan tare da kasancewa a ankare da duk wani motsi da ba su gamsu da shi a wurarensu, kamar wuraren ibada da kasuwanni da masarautu da makarantu da sauran wuraren taruwar jama'a.
Hukumar ta yi kira ga masu kula da wadannan wurare da su yi ƙoƙarin kai rahoto ga hukumomin tsaro kan duk abin da ba su gamsu da shi ba.
Ta ce shafin intanet ɗinta da layukan wayarta na kai ƙorafi za su kasance a buɗe ga al'umma.
Kula da yara a lokacin hutu
A yayin da makarantu suka yi hutu ɗalibai suka koma gida don yin hutu, akwai yiwuwar ɓata-gari za su yi ƙoƙarin sanya su cikin munanan ayyukansu in ji hukumar DSS.
Ta lissafa 'munanan abubuwa' kamar su sata da fashi da rashin ɗa'a da zanga-zanga da shaye-shayen munanan ƙwayoyi da satar mutane kan kuɗin fansa.
A don haka ne hukumar ta yi kira ga iyaye da su sa ido kan ayyukan da Æ´aÆ´ansu ke aikatawa don hana su yin abubuwan da ba su dace ba.
"Baya ga É—alibai, Æ´an majalisar jihohi da na tarayya da ma'aikatan gwamnati da na kamfanoni ma da ke hutu na iya fuskantar barazana da dama.
"Wannan ya kuma shafi ƴan Najeriya da mai yiwuwa su yi tafiye-tafiye a ciki da wajen ƙasar don yin bukukuwan tare da su."
GargaÉ—i ga masu satar mutane
WaÉ—ancan mutanen na sama da hukumar ta yi magana a kansu na iya fuskantar barazanar sace su da kashe su ko kuma amfani da su a siyasance ta hanyar da ba ta dace ba, in ji DSS.
"Don haka muna kira a gare su da su zama masu taka tsantsan ta yadda ba za su faÉ—a hannun waÉ—ancan bara-gurbin ba."
DSS ta jaddada gargaÉ—inta ga Æ´an bindiga da masu satar mutane da Æ´an ta'adda da dukkan wasu masu kai hari kan hukumomin tsaro da fararen hula da cewa gara su sake tunanin.
"Waɗannan mutanen walau a arewa suke ko a kudu sun san kansu. Babu shakka sun tsallake iyakoki kuma yanzu lokaci ya yi da za a murƙushe su."
Batun Nnamdi Kanu
Hukumar DSS ta kuma taɓo batun jagoran ƴan awaren Biafra wato Nnamdi Kanu, inda ta musanta batutuwan da ake cewa tana gallaza masa a yayin da yake tsare.
"A baya ba ma magana ne kan Kanu ba don tsoron kowa ko komai ba sai don gudun jawo ce-ce-ku-ce. Amma a yanzu albarkacin ƙeƙe da ƙeƙe da girmama dimokraɗiyya ne hukumar taken son fayyace abubuwa."
- DSS ta yi watsi da zargin cewa tana muzgunawa Kanu
- An samar masa da dukkan kayan alatun da yake buƙata irin wanda ba za a same su a ko ina ba a faɗin ƙasar
- An ba shi cikakkiyar damarsa Æ´ancinsa
- Ba a taɓa hana shi damar ibada ba
- Ana ba shi damar ganin ƙwararrun likitoci masu duba lafiyarsa. "Shi da kansa Kanu ya tabbatarwa da masu ziyartarsa cewa ba a taɓa muzguna masa ba."
- Maganar cewa ana barinsa da yunwa ma ƙage ne. Abinci sai wanda ya zaɓa ake ba shi.
- Batun ba a barinsa ya sauya kaya ƙarya ne.
Kafafen yaÉ—a labarai
Sanarwar ba ta kammala ba sai da ta taɓo kafafen yaɗa labarai ta hanyar tunatar da su aikinsu a fannin tsaron ƙasa.
Ta yi kira ga Æ´an jarida a matsayinsu na masu faÉ—a a ji da su yi amfani da kafafensu wajen samar da zaman lafiya.
"Dole su mayar da hankali wajen haɗin kan ƙasa da gujewa labaran ƙarya da na tunzuri da kalaman ƙiyayya.
"Dole ƴan jarida su zama masu kishin ƙasa da yin komai bisa gaskiya a rahotanninsu."
Sauran ƴan ƙasa
Su ma sauran ƴan ƙasa hukumar DSS ta nemi da su haɗa kai da hukumon tsaro don tabbatar da zaman lafiya a ƙasar.
Su kuma guji yaɗa duk wani abu da zai jawo karyewar doka da oda. Sannan su lira da ayyukan da zau aiwatar a lokutan bukukuwan ƙarshen shekara.
Baya ga dukkan gargaɗin da hukumar tsaro ta farin kayan ta bayyana, a ƙarshe ta ce ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen ɗaukar mataki kan duk wanda ya so kawo cikas ga zaman lafiya da tsaron ƙasa kamar yadda doka ta tanada.
No comments