Daga Abubakar M Tahir Hadejia Kungiyar Ci gaban garin Auyo mai Suna Auyo Concerned Citizens Forum (ACCF) a turance ta gudanar da...
Daga Abubakar M Tahir Hadejia
Kungiyar Ci gaban garin Auyo mai Suna Auyo Concerned Citizens Forum (ACCF) a turance ta gudanar da babban taron shekarar 2021 a dakin taron dake Sakatariyar mulki ta karamar hukumar.
Taron wanda aka fara shi ranar Lahadi 26 ga watan Disamba wanda aka karkare shi 27 ga wata ya samu halartar dimbin al'ummar yanki, Æ´an siyasa, masu Sarauta, Æ´an kasuwa dama Æ´an bokon garin.
Da farko an fara da gabatar da Ƙasida mai dauke da manufofin Zauren dama nasarorin daya samu wanda shugaban Kungiyar Injiniya Garba Adamu ya gabatar.
Cikin jawabin nasa Injiniya Garba Adamu ya bayyana cewa, sun kafa zauren ne a shekarar 2016 wanda ya zama inuwa ga duk wani mazaunin yankin, inda zuwa yanzu sun sami nasarar mallakar shaida daga CAC.
Ya kara da cewa ya zuwa yanzu sun sami nasarar hada kan membobin kungiyar dake fadin kasarnan. Sun kuma sami manyan nasarori ciki kuwa harda Ci gaban aikin Hadejia-Ja'amare dama TRIMMING.
Injiniya Garba ya kara da cewa babban burinsu shi ne samar da daidaito a tsakanin Æ´an siyasar yankin.
Shima a nasa jawabin Hakimin Auyo Alhaji Umar Muhammad Baffa ya nuna matukar farin cikinsa kan wannan kokari na Zauren ACCF.
Inda ya ce suna sa ran zuwa gaba yankin na Auyo ya zama cikin sahun gaba da ake alfahari da su ta fuska ilimi da sauran bangarorin rayuwa, a jihar Jigawa da kasa baki daya.
Hakimi Auyo ya kuma bukaci membobin kungiyar da su zama masu hakuri saboda gudanar da irin wannan tafiya sai an daure a kuma yi don Allah.
Shima a nasa jawabin Shugaban Karamar Hukumar Auyo Alhaji Muhammad Baffa Shinge ya yi Alkawarin samarwa zauren na ACCF Sakateriya a ko'ina ne a garin Auyo domin samar da cigaban yankin.
Baffa ya kara da cewa a shirye suke su bada dukkanin gudummawar da ta dace domin ci gaban yankin.
Dayake gabatar da muƙala Mai Taken "kalubalen tsaro da mafitarsa", D.P.O na Garin Auyo ya kawo jerin matsalolin tsaro da suka addabi Arewacin jasar nan, inda ya bayyana cewa Hukumar ƴan sanda a shirye take wajen shawo kan matsaloli.
Ya kuma nuna jin dadinsa kan yadda zaman lafiya ya samu a jihar Jigawa.
Al'ummar da suka halarci wannan babban taro sun nuna jin dadinsu da irin namijin kokarin zauren domin samarwa da garin na Auyo mafita me cike da cigaba ta fuskar Zamani.
No comments