Shugaban hukumar bunƙasa fasahar sadarwa (NITDA) Malam Kashifu Inuwa a taron. Daga Abubakar M Tahir Kungiyar Tsofaffin Da...
Shugaban hukumar bunƙasa fasahar sadarwa (NITDA) Malam Kashifu Inuwa a taron.
Daga Abubakar M Tahir
Kungiyar Tsofaffin Daliban Makarantar Sakandaren kimiyya da fasaha dake garin Kafin Hausa aji na 1997 ta gudanar da babban taron ta na shekara a makarantar koyon jinya dake garin Hadejia.
Taron da ya samu halartar ƴan kungiyar daga jihohi Kano, Jigawa, Yobe da Bauchi ya samu halartar shugaban hukumar bunƙasa fasahar sadarwa (NITDA) Malam Kashifu Inuwa da dan majalisa mai wakiltar mazabar Gumel.
Da yake jawabi ga manema labarai, Shugaban hukumar NITDA Malam Kashifu Inuwa ya bayyana cewa sun saba gudanar da wannan taro duk shekara wanda suke yin zumunci da junansu su kuma tallafi marasa ƙarfin cikinsu.
Malam Kashifu Inuwa ya kara da cewa ya ji dadin taron na bana ganin irin tallafin da suka bai wa ƴan kungiyar masu karafin karfi.
Kashifu ya kara da cewa Kungiyar KAHOSSA 97 ba ta tsaya nan ba, takan lura da halin da makarantar take ciki ta tallafa mata.
Da yake jawabi Sakataren Kungiyar Malam Isa Umar Muhammad Bulangu ya zayyano irin nasarorin da suka samu wanda ya haɗa da samar da hadin kai ga ƴan kungiyar.
Isar Umar ya kara da cewa sun gabatar da kyautar Naira dubu dari ga membobin guda tara da suka fito daga garuruwa domin inganta sana'o'insu.
Da yake jawabin godiya Shugaban kungiyar ta KAHOSSA 97 Mallam Muhammad Bashir Dauda Hadejia ya bayyana matuƙar farin cikinsa ga yadda taron ya gudana lafiya.
Malam Dauda ya kara da cewa tunda aka kafa makarantar Kimiyya dake Kafin Hausa babu wata kungiya dake gudanar da ayyukan cigaba kamar ta su.
A karshe ya yi addu'a Allah ya sakawa kowa da alkhairi ya maida kowa gida lafiya.
No comments