Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta Nijeriya, NCDC ta bayyana cewa, cutar kwalara ta fi kashe jama’a fiye da annobar korona...
Hukumar
Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta Nijeriya, NCDC ta bayyana cewa, cutar kwalara
ta fi kashe jama’a fiye da annobar korona musamman a wannan shekara ta 2021 a
kasar.
Darakta
Janar na Cibiyar ta NCDC, Ifedayi
Adetifa ya bayyana cewa, Nijeriya ta samu adadin mutanen da ya zarta dubu 3 da 600 da suka rasa rayukansu a
dalilin annnobar amai da gudawa ko kuma kwalara a cikin watanni 11 da suka
gabata.
A
game da annobar korona kuwa, kimanin mutane dubu 2 da 977 ne suka rasa
rayukansu tun daga farkon shekarar bara zuwa wannan lokaci, kamar yadda Mista
Adetifa ya yi karin bayani.
Jami’in
na hukumar NCDC na bayani ne a yayin wata hira da ya yi da kafar Talabijin ta
Channels, inda ya yi bayani game da
sabon nau’in cutar korona da ake kira Omicron da ya bulla a Nijeriya.
A
cewarsa, yanzu haka sun dukufa ne wajen takaita yaduwar cutar kwalara duk da
cewa, a halin yanzu, mutane sun fi karkata hankulansu kan annobar korona.
A
bangare guda, Mista Adetifa ya kara a
cewa, tuni suka fara kintsawa domin tunkarar kakar ciwon sankarau, yana mai
cewa, sun tanadi ma’aikata tare da horas da su don gudanar da aikinsu na wayar
da kan al’umma.
No comments