Kwastam Ta Cafke Bama-bamai Da Aka Shigo Da Su Daga Kasashen Ketare


Hukumar Kwastam da ke tashar jirgin sama ta Murtala Muhammad ta kasa da kasa da ke a Legas, ta kama wasu bama-baman da aka shigo da su daga kasashen ketare.

Rundunar ta kuma kama miyagun kwayoyi na tramadol na miliyoyin naira.

Ana zargin wasu kamfanoni ne suka shigo da maganin da a wasu lokuta ana shigo da su kana su fada a hannun miyagun mutane a Nijeriya.

Tuni aka mika ababen fashewa ga rundunar 'yan sandan Nijeriya.

Post a Comment

0 Comments