Alexandre Lacazette ya ki amincewa da tayin tsawaita yarjejeniyarsa da Arsenal da tsawon shekara 1, matakin da jaridar L’Equipe ta Faransa...
Alexandre Lacazette ya ki amincewa
da tayin tsawaita yarjejeniyarsa da Arsenal da tsawon shekara 1, matakin da
jaridar L’Equipe ta Faransa ta danganta da shawarar da dan wasan ya yanke ta
neman sauyin sheka karakshin yarjejeniya mai tsawo.
Shawarar da Lacazette ya yanke dai
ta zamewa mai horas da Arsenal Mikel Arteta kalubale gabanin kasuwar musayar
'yan wasa a watan Janairu, la'akari da cewar dan awsan na daga cikin zakakuran
'yan gaba da kocin ke alfahari da su.
Lacazette ya taka rawar gani a
Arsenal a 'yan watannin nan, ciki har da cike gurbin kaftin na Pierre-Emerick
Aubameyang wanda Arteta ya karbe jagorancin tawagar ‘yan wasansa daga
hannunshi.
Kawo yanzu kwallaye 53 Lacazette ya
ci wa Arsenal cikin wasanni 42 da ya bugawa kungiyar.
No comments