Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

MAAUN Ta Nemi Wadanda Ke Neman Jami'ar Su Dora Sakamakon Jarabawarsu

Jami'ar Maryam Abacha American University ta Nijeriya dake Kano na sanar da dukkanin waɗanda suka sanya Jami'ar Maryam A...


Jami'ar Maryam Abacha American University ta Nijeriya dake Kano na sanar da dukkanin waɗanda suka sanya Jami'ar Maryam Abacha American University na Nijeriya a matsayin zabinsu na farko a  jarabawar da hukumar shirya jarabawar shiga jami’a (JAMB) ta kammala a kwanan nan, da su je kowacce cibiyar CBT su dora sakamakon jarabawarsu ta kammala Sakandire kafin a ci gaba tantance bukatar su ta shiga Jam'iar.

Sanarwar ta musamman ta fito ne daga hukumar Jami'ar a takardar da ta sanyawa hannu a ranar Talata. 

Hukumar ta kara da cewa; "Abu na biyu, wadanda suke son shiga Jami'ar za su iya yin hakan ta hanyar sayan 'Green Card' daga CBT mafi kusa da su domin sauya Jami'a tare da sanya sakamakon jarabawarsu."

No comments