Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Matasa 1700 Ne Suka Sami Tallafin Honorabul Babawo A Karamar Hukumar Sabon Gari

Daga A'isha Suleman, Zariya Dan Majalisar Tarayya Mai Wakiltar Mazabar Sabon Gari kuma Shugaban Kwamitin Hukumar Kula Da Har...Daga A'isha Suleman, Zariya

Dan Majalisar Tarayya Mai Wakiltar Mazabar Sabon Gari kuma Shugaban Kwamitin Hukumar Kula Da Harkokin Jiragen Ruwa a Majalisar Wakilai Honorabul Garba Datti Muhammad (Babawo) ya dauki nauyin horar da matasa mata da maza 1700 a Karamar Hukumar Sabon Gari akan sana'o'i daban-daban.

Wakiliyarmu ta ziyarci wuraren da aka gudanar da horon kuma ta aiko da yadda lamarin ya gudana kamar haka.

Shirin an fara shi ne a tsawon kwanaki masu yawa zuwa ranar Alhamis 23 ga watan Disambar 2021 kuma an kammala duk horon a cikin tsari da nasara.

Wannan horo ya gudana ne a TJ Hotel da RAS Event Centre da Dove Event Centre da kuma Cibiyar NEARLS A.B.U. Samaru duk a karamar Hukumar Sabon Gari.

Daga cikin sana'o'i da aka koyar a wannan lokacin akwai koyan kiwon Kaji akwai koyan dafa abinci da sauran kananan sana'o'i daban daban da mutum zai iya rike kansa da kansa.

Bayan kammala samun horon ne kowane mahalarci ya sami takardar shahada (Certificate) da kuma tallafin kudi na naira dubu ashirin da biyar domin su jà jari.

Halima Yusuf daga mazabar Samaru kuma tana cikin wadanda suka sami horo a bangaren dafa abinci ta shaidawa jaridarmu cewa sun sami horo kuma sun ji dadi kuma za su yi amfani da ilmin da suka samu a hanyar da ta dace. Karshe Malama Halima ta yi fatan Allah ya biya Honorabul Garba Datti Babawo da alheri ya biya masa bukatunsa duniya da lahira.

Malam Muhammad daga mazabar Chikaji ya sami horon ne a bangaren kiwon kaji shima ya nuna farin cikinsa da wannan tallafin ilmi da kudi na fara sana'a domin haka ya yi fatan Allah ya biya Dan majalisa Babawo da alheri mai yawa karshe ya yi kira da sauran 'yan siyasa da su yi koyi da hali irin na mai girma Honorabul Garba Datti Babawo.

Malam Nass da Malam A.D.O Samaru da Honorabul Sani Basawa da Alhaji Uwaisu da Malam Babawo karami dukkansu mutane ne masu taimakawa Dan majalisar a bangaren ci gaban siyasarsa kuma suna cikin wadanda suka gudanar aikin karkashin cibiyar CMD ta kasa wato Canter For management Development.

An yi taro lafiya an tashi lafiya.

No comments