Daga Abubakar M Tahir Shugaban Hukumar Bunƙasa fasahar sadarwa ta ƙasa(NITDA) Malam Khashifu Inuwa Abdullahi yayi kira na musamm...
Daga Abubakar M Tahir
Shugaban Hukumar Bunƙasa fasahar sadarwa ta ƙasa(NITDA) Malam Khashifu Inuwa Abdullahi yayi kira na musamman ga matasa kan muhimmancin amfani da kafafen sadarwa zumunta wajen neman rufin asiri.
Cikin Wata ganawa da yayi da manema labarai a lokacin hutun Kirisimeti,
Daraktan ya bayyana cewa Kamfanonin Sadarwa sunfi kowane kamfani kudi a duniya.
Hanyar da suke samun kudaden itace amfani damu, me zai hana muma bazamu yi amfani dasu wajen samun kuÉ—i ba.
Malam Khashifu Inuwa ya kara da cewa Hukumar su ta dukufa wajen wayar da kan matasan Kasar nan muhimmanci kafafen sadarwa inda a cikin Shekarar 2021 suka gudanar da horo ga matasa dubu sha daya a jihohin kasar nan sha bakwai.
Dayake bayyana irin nasarar da hukumar sa ta NITDA ta Samu,
Mallam Khashifu Inuwa ya bayyana cewa yanzu haka sun kirkiri tsaruka guda uku wanda suka haÉ—a da sarrafa fasahar da Allah ya hore maka wato (productivity), da kuma tsarin (Digital Content creation) yadda zaka yi rubutu mai ma'ana Wanda mutane zasu amfana.
Daga nan sai tsarin Digital Marketing wato hada-hadar kasuwanci ta yanar Gizo wanda mutum zai iya kirkirar tallace-tallace ya kuma sigar dasu cikin miliyoyin kudi.
A karshe Malam Khashifu ya kara nuna farin cikinsa kan nasarorin da hukumar take samu a shekara ashirin daga kirkirar ta.
No comments