Daga Bilal Nasir Umar Sakkwato Almajiran Shaikh Ibraheem Zakzaky na Sakkwato sun gudanar da gangami tare da yin kiraye-kiraye da...
Daga Bilal Nasir Umar Sakkwato
Almajiran Shaikh Ibraheem Zakzaky na Sakkwato sun gudanar da gangami tare da yin kiraye-kiraye dangane da kashe-kashen da yake faruwa a Arewacin kasarnan.
Taron gangamin ya gudana ne da yammacin ranar Juma'a 10 ga watan Disamba shekara ta 2021.
Wakilin 'yan'uwa Musulmi almajiran Shaikh Zakzaky na yankin Sakkwato, Shaikh Sidi Munir ne ya jagoranci wannan gangamin, ya kuma gabatar da takaitaccen jawabi dangane da fitowar ta su, inda ya ce sun fito ne domin nuna rashin amincewa da abubuwan da suke faruwa a Arewacin kasarnan na kashe-kashen al'ummar Musulmi babu gaira babu sabab.
No comments