Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Me Yafi Wannan Haushi Ka Rushe Abin Da Ka Gina Da Kuɗinka? Daga Mustapha Muhammad

Kamar yadda sanarwa daga Gwamnatin Jihar Kaduna ta riski ragowar al'ummar da ba a rushe musu shaguna ba, wanda sune daman ɓa...Kamar yadda sanarwa daga Gwamnatin Jihar Kaduna ta riski ragowar al'ummar da ba a rushe musu shaguna ba, wanda sune daman ɓangaren da ya rage ba a ƙaraso kansu ba a cikin kasuwar Sabon Garin Zariya wajen rushe kasuwa da ake yi da kuma gyarawa ƙarƙashin kulawar Gwamna Nasiru El'rufa'i. 

A satin da ya gabata ne aka aikowa wannan ɓangare da ya rage ba a rushe ba da notis na tashi a wajen nan da kwanaki bakwai (7). 

Tun ranar Lahadin da ta gabata ne al'ummar da aka aikowa notis a wajen suka fara kwashe kayayyakin su domin tsira da wasu abubuwa nasu. Masu shaguna ginannu kuma suka fara rushe shagunan su da hannunsu domin su tsira da wasu abubuwa, kada asarar ta yi yawa.

Zaka sha mamaki sannan zaka tausayawa al'umma idan kaje wajen ka ga yadda suka mayar da hankali wajen rushe shagunan, hakan yana da alaƙa da yadda Gwamnatin ke dirar mikiya ko da lokaci bai cika ba, su lalata dukiyar al'umma, a gefe guda kuma wasu daga cikin 'talakawa' su sace maka kaya da sunan ganima. Dalilin haka ne yasa al'umma ke rushe shagunan su tun kafin gwamnati ta turo a rushe shagunan nasu.

Shagunan da Gwamnatin Jihar Kaduna ta gina kuma ga tsada mai ƙaramin Jari ba zai iya kama shago ba. Sai dai masu ƙarfin Jari ne kawai za su iya kamawa. Shi kuma mai ƙaramin jari an rusa shi ke nan, sai dai ya fita kasuwar ko kuma ya fara rara-gefe a cikin kasuwar. 

Wannan wani irin ƙalubale ne da masu ƙaramin ƙarfi suke fuskanta a cikin kasuwar Sabon Garin Zariya ta jihar.

No comments