Daga Umar Shuaibu Falsafar kyawawan halaye ko ɗa'a (moral or ethical philosophy) wani ɓangare ne na falsafa da ke yin nazari...
Daga Umar Shuaibu
Falsafar kyawawan halaye ko ɗa'a (moral or ethical philosophy) wani ɓangare ne na falsafa da ke yin nazari a kan dacewa ko rashin dacewar wani aiki ko al'amari, kyawun hali ko munin shi, halin kirki ko saɓanin shi da kuma adalci ko zalunci.
A falsafar kyawawan halaye, muna da nazarori daban-daban da suke bayani a kan matsayi da ma'aunan da ake auna Halayen mutane sannan a danganta su da kyau ko muni. Kamar dai yadda muke da kyawawan dabi'u da kuma munana.
Me ke sa wa a ce wannan dabi'a na da kyau ko muni?
Shin kyawawan dabi'u gama gari ne ko dai ko wani yanki na Duniya na da na su kyawawan dabi'un daban?
Masana halayya da zamantakewa sun fitar da nazarori daban-daban domin amsa tambayoyin da ke sama.
A fahimtar wasu masana, mutanen wani yanki ne ke zama su fitar da doka cewa, hali kaza bai da kyau, duk wanda ya aikata shi za a mishi irin hukunci kaza. ÆŠabi'a iri kaza kuma na da kyau, wanda ya aikata shi mutumin kirki ne abin girmamawa.
Wasu kuma sun tafi a kan cewa, kyawawan halaye ba su keɓanci wani yanki ko kaɓila ba, a'a, kyawawan halaye ko nagarta duk Duniya abin amincewa ne. Misali, Babu wani lungu da mutum zai je a Duniyar nan a ce mishi Sata na da kyau ko Zalunci na da kyau.
Akwai kuma masu auna nagarta ko rashin sa bisa doron ra'ayin ƙashin kai, wanda a takaice abinda suke nufi shine, abinda kawai na dauka yana da nagarta shine mai nagarta, kuma abu mai nagarta ya kan iya rasa nagarta idan na sauya ra'ayi na a kan shi. Misali, Saurayi yayi ta kururuta nagartar budurwar shi a lokacin da suke soyayya, amma idan wani ya zo ya kasa shi, ya aure ta sai ya koma cewa ai dama ba ta da nagarta, wanda kuma a hakikanin gaskiya ba lallai ya zama haka ba.
Zai yiwu tun farko ma ba nagartar take da shi ba, kawai saboda yana son ta ne yake danganta mata nagarta. Zai yiwu kuma tana da nagartar, sakacin shi ne yasa ya rasa ta.
Haka nan banbanta tsakanin karya da gaskiya, hali mai kyau ko mai muni, su ma da haka suke kasafta su. Suna gane mutum na da gaskiya ne ba tare da duba me yake cewa ba, kawai idan su ka ga mai maganar a garin su yake, ko addinin su, ko ɓangaren su yake shikenan abinda ya ce ya zama gaskiya. Haka kuma idan suna da saɓani da mutum ko me yace ya zama Ƙarya. Kamar dai yadda da yawan mu 'yan Nijeriya muke, musamman mu da ke arewacin kasar.
Idan muka yi duba ga wannan nazarin da idon basira za mu ga cewa a maimakon su tabbatar da nagarta da kuma fifikon nagarta a kan rashin sa, su kuma ware halayen kirki daga gurbatattu suna kokarin kore fifikon nagarta ne ma (ko sun sani ko ba su sani ba).
Domin ra'ayin ƙashin kai a kan kanshi bai da wani daraja ko fifiko, don yau na ce a ra'ayi na, na fi son tuwon masara da miyan kuka a kan shinkafa da miya ba shi ke nuna cewa tuwon masara da miyan kuka ya fi shinkafa da miya fifiko ba.
Dole mu ko yi fifita gaskiya a kan ra'ayin kan mu, ko da wanda ba ma so ne yake da nagarta, mu ba shi fifikon nagartar da yake da ita hakan shi ne adalci. Kuma hakan zai kara yawan masu nagarta a cikin al'umma.
No comments