Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

Mummunan Hatsari Ya Sabbaba Rufe Hanyar Gidan Sarkin Dukku Ta Jihar Gombe

Daga Umar Babagoro A jiya Laraba 1 ga watan Disambar 2021 wani mai Babur ya buge wani Dattijo mai suna Malam Adamu D.A. Hatsarin...


Daga Umar Babagoro

A jiya Laraba 1 ga watan Disambar 2021 wani mai Babur ya buge wani Dattijo mai suna Malam Adamu D.A. Hatsarin ya auku ne bayan sallar azahar dab da kofar gidan Mai Martaba Sarkin Dukku Alhaji Haruna Rashid II. Munin hatsarin ya sabbaba rufe hanyar domin a samu damar wanke jinin da ya malale kan hanyar. 

Shaidun gani da ido sun bayyana gudun mai Babur din a matsayin musabbabin wannan hatsari, sai dai wasu sun ce mai Babur din yana sauri ne domin ya kai inda yake harin kai wa a dan karamin lokaci.

                  Dattijon da aka buge

Wakilinmu ya je dakin Accident/Emergency dake Babban Asibitin Dukku, inda ya iske duk gidajen dakin a cike da masu raunukan hatsarurukan Babur daga wurare daban-daban, wanda hatsarurrukan suke da dangantaka da yawan gudun masu babura, da kuma tukin ganganci.

Idan ba a manta ba a ranar Asabar 27 ga watan Nuwamban 2021 da ta gabata an sallaci gawarwakin mutane hudu (4) a babba Asibitin Dukku, wanda Babura suka yi sanadiyyar rasuwarsu.

 Mai babur din ya samu mummunan rauni

No comments