Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

NCDC Ta ce Zazzabin Lassa Na Ci Gaba Da Kisa A Nijeriya

An sake samun wadanda suka mutu sanadiyar cutar zazzabin Lassa a jihohi biyu na Najeriya. Hakan na nufin adadin mutanen da suka ...


An sake samun wadanda suka mutu sanadiyar cutar zazzabin Lassa a jihohi biyu na Najeriya.

Hakan na nufin adadin mutanen da suka mutu sakamakon cutar tun daga farkon shekarar 2021 zuwa yanzu ya kai mutum 92.

Sabon rahoton hukumar da ke yaki da cutuka masu yaduwa a Najeriya NCDC ya ce ya zuwa yanzu, mutum 454 ne suka harbu da zazzaɓin a kananan hukumomi 66 da ke jiha 16 na faɗin Najeriya, hadi kuma da Abuja babban birnin ƙasar.

Jihohi uku daga ciki da suka haÉ—a da Edo (197) da Ondo (159) da Taraba (21) ne ke da kashi 83 cikin 100 na dukkan mutanen da aka tabbatar sun kamun.

Sai kuma jihohin Bauchi da Ebonyi masu mutum 18 kowaccensu, a cewar NCDC.

A mace-macen da aka samu a baya bayan nan kuwa, rahoton na NCDC ya nuna cewa an samu karin mutum uku da suka mutu sakamakon cutar.

Jihar Bauchin a Arewacin Najeriyar na daga cikin jihohin da NCDC tace cutar ta dawo har ma a na hasashen ta zo da ajali ga wasu da ta kama.

Dr. Sama'ila Dahuwa shi ne kwamishinan lafiya na jihar Bauchin, ya kuma fada wa BBC cewa an samu bullar cutar a kananan hukumomin Tafawa Balewa da Bagwaro da Torro da kuma Kirfi.

"Hakika muna da rahotanni namu na cikin gida da suka tabbatar da barkewar wannan cuta a kananan hukumomi guda hudu." In ji Dr Dahuwa.

Ya kara da cewa "maganar mutuwa ba mu tabbatar ba amma muna kan bincike, don mutanen ma da mu ke jin cewa sun mutu sun ma fi mutum uku, to amma bamu tabbatar ba idan mun tabbatar za mu yi bayani." In ji kwamishinan lafiyar.

Hukumomin lafiya a Najeriya sun bayyana hadarin da ke tattare da cutar zazzabin Lassa, da ya hada da zazzabi mai zafi, da amai, da kuma fitar jini ta kafofin jikin mutum.

Dr Hassan Garba wani kwararren likita ne a Najeriya, kuma ya fada wa BBC cewa "hatsarin cutar Lassa akwai zazzabi, ta kan iya sa amai, amma babban hatsarin shine fitar jini ta kunne da hanci. Ko kuma mace ba jinin al'ada take ba amma ta rika zubar da jini." In ji Dr Garba.

Bugu da kari likitan ya bayyana cewa Lassa cuta ce da ke saurin kisa, kuma ta samo asali ne daga wani nau'in beraye mai nono da yawa da ake kira 'multi mermaid' da yaren Ingilishi.

A kan haka ya bukaci al'umma da su guji barin beraye kusa da su ko kuma taba abubuwan da suke amfani da su, kuma su garzaya asibiti da zarar sun fahimci alamun cutar tare da su ko wani makusancinsu.

Karuwar masu kamuwa da cutar zazzabin Lassa a Najeriya na zuwa ne a dai-dai lokacin da kasar ke fuskantar karuwar masu kamuwa da cutar korona.

No comments