Tsohon kocin Super Eagles Gernot Rohr ya ce hukumar kwallon kafar Nijeriya ta NFF ba ta yi masa adalci da ta kore shi ba, yana m...
Tsohon kocin Super Eagles Gernot Rohr ya ce hukumar kwallon kafar Nijeriya ta NFF ba ta yi masa adalci da ta kore shi ba, yana mai cewa kungiyar na taka rawar a zo a gani karkashin jagorancinsa.
A farkon makon nan hukumar ta NFF ta sallami Rohr ta maye gurbinsa da tsohon kyaftin din Super Eagles Augustine Eguaveon.
Sai dai a wata hira da ya yi da ESPN, Rohr ya nuna rashin jin dadinsa dangane da matakin sallamar shi da aka yi, inda ya ce ya cika duka burukan da aka gindaya masa wajen ciyar da kungiyar gaba.
A cewar Rohr, bai kamata a ce hukumar ta NFF ta dauki wannan mataki gab da za a fara gasar cin kofin nahiyar Afirka ba.
A shekarar 2016 aka nada Rohr a matsayin kocin Super Eagles, shi ne kuma kocin da ya fi dadewa a wannan mukami.
No comments