Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

Nijar Ta Kori Mutanen Da Suka Yi Kisa A Rwanda

Mahukuntan Jamhuriyar Nijar sun kori ‘yan asalin kasar Rwanda su 8 da aka zarga da hannu a  kisan kiyashin kasar na shekarar 199...Mahukuntan Jamhuriyar Nijar sun kori ‘yan asalin kasar Rwanda su 8 da aka zarga da hannu a  kisan kiyashin kasar na shekarar 1994 bayan share tsawon makonni da isar su birnin Yamai babban birnin kasar.

Wata sanarwa da Ministan Cikin Gidan Jamhuriyar Nijar Hamadou Amadou Souley ya sanya wa hannu, ta nuna cewa an bai wa mutanen 8 umurnin ficewa daga kasar saboda dalilai na diflomasiyya, lura da cewa yanzu haka mutanen na cikin jerin wadanda kotun duniya ta musamman da aka kafa don hukunta masu hannu a rikicin Rwanda ke nema ruwa a jallo.

Tuni kungiyar agaza wa mutanen da rikicin Rwanda ya rutsa da su, ta yi lale marhabin da matakin da Nijar ta dauka, tana mai cewa, hakan tamkar izina ce ga sauran masu hannu a kisan kare dangin wadanda kuma ake nema domin hukunta su kamar yadda RFI ta labarto.

Bayanai na cewa, gwamnatin Nijar ta kori wadannan mutane ne bayan takwararta ta Rwanda ta nuna fushinta karara kan yadda aka ba su mafaka a Yamai kamar yadda jaridar Jeune Afrique ta rawaito.

Sanarwar da Ministan Cikin Gidan Nijar din ya fitar, ta ce, daga yanzu, an haramta wa mutanen zama na din-din-din a kasar saboda dalilai na diflomasiya.

No comments