Ma’aikatar Matasa da Wasanni ta Nijeriya ta amince wa Hukumar Kwallon Kafar Kasar da ta kori kocin tawagar Super Eagles Gernot R...
Ma’aikatar Matasa da Wasanni ta Nijeriya ta amince wa Hukumar Kwallon Kafar Kasar da ta kori kocin tawagar Super Eagles Gernot Rohr tare da gaggauta dauko kwararren da zai maye gurbinsa.
Umarnin
Ma’aikatar na zuwa ne bayan wata ganawa da ta gudana tsakanin Ministan Wasanni
da Matasana Sunday Dare da kuma shugaban Hukumar Kwallon Kafa ta kasar, Amaju
Pinnick a birnin Abuja a jiya Alhamis.
Sai
dai sharadin da Ministan ya bai wa NFF shi ne ta tabbatar da cewa ta biya Rohr
daukacin hakkokinsa ko kuma wani kaso mai yawa daga cikin hakkopkin kafin ta
dauko sabon kocin Super Eagles.
Wannan
na zuwa ne a daidai lokacin da aka zafafa kiraye-kirayen hukumar ta NFF da ta
gaggauta sallamar kocin, saboda rashin
tabuka abin kirki musamman a wasannin baya-baya nan na neman tikikin
halartar gasar cin kofin duniya a Qatar.
Tuni
wasu daga cikin ‘yan Najeriya suka fara bada shawarar daukar Emmanuel Amunike
tare da Salisu Yusuf don jagorantar
tawagar ta Super Eagles.
(RFI)
No comments