Miliyoyin al’umma a sassan duniya na shirin gudanar da bikin Kirismati a daidai lokacin da sabon nau’in cutar Korona na Omicron ke ci gab...
Miliyoyin al’umma a sassan duniya na shirin gudanar da
bikin Kirismati a daidai lokacin da sabon nau’in cutar Korona na Omicron ke ci
gaba da yaduwa, lamarin da ake ganin zai rage armashin bikin a bana.
RFI ta labarto cewa; kodayake
akwai mutane da dama da za su gudanar da bikin na Kirismati a killace a gidansu
domin kauce wa kamuwa da annobar ta Korona, nau’in Omicron wanda aka ce yana da
wuyan sha’ani.
Shekaru
biyu kenan jere da juna da wannan annoba ta Korona ke haifar da cikas ga bikin
na Kirismati.
A
can Bethlehem kuwa, wurin da mabiya addinin Kitrista suka yi amanna cewa, nan
ne mahaifar Annabi Isa Alaihi-s-salatu wassalam, masu gidajen otel-otel sun
shiga damuwa saboda karancin baki da cutar ta Korona ta takaita adadinsu a
bana, yayin da kuma Isra’ila ta rufe kan iyakokinta.
A
tsakar daren yau Juma’a, wato jajibirin ranar bikin na Kirismatin, tsirarun
mutane ne za su gudanar da taron addu’a a birnin na Bethlehem, al’amarin da ba
a saba ganin haka ba.
Gwamnatocin
kasashen Turai sun kafa wasu tsauraran ka’idojin yaki da cutar ta Korona,
lamarin da ya rage wa bikin na Kiristamatio armashi.
Kasashe
irinsu Netherlands da Spain da Italiya duk sun wajabta sanya takunkumin rufe
baki da hanci musamman a bainar jama’a da zummar takaita yaduwar annobar a
lokacin bikin na Kirismati.
No comments