Wani rahoto da wata cibiyar tattara bayanan sirri ta SB Morgen Intelligence ta wallafa ta ce an kashe jami'an tsaro a Naje...
Wani rahoto da wata cibiyar tattara bayanan sirri ta SB Morgen Intelligence ta wallafa ta ce an kashe jami'an tsaro a Najeriya da suka kai 966 a shekara guda.
Cibiyar ta saki rahoton ne a ranar Alhamis, bayan tattara bayanan sirrin da ta yi na hare-hare da aka kai wa jami'an tsaro daga watan Oktoban 2020 zuwa Satumbar 2021.
Rahoton ya bayyana ma'anar yaƙi a matsayin duk wani rikici da aka kashe mutum aƙalla 1,000. "Saboda wannan za mu iya cewa Najeriya na cikin yaƙi," a cewar rahoton.
Zuwa yanzu babu wani martani daga hukumomin tsaron Najeriya game da rahoto.
Alƙalumman rahoton na SB Morgan sun bayyana cewa an kashe sojoji 642 da ƴan sanda 322 a cikin hare-haren da 'yan bindiga suka kai wa jami'an tsaro a cikin watanni 12.
An kuma kashe jami'an tsaron kare fararen hula na Civil Defence 11 na jami'an hukumar kwastan biyar da DSS biyu da jami'an shige da fice guda biyu da jami'in hukumar kiyaye haɗurra guda.
Rahoton ya kuma ce na kashe a kalla 'yan bindiga 1,989, yayin da aka kashe mayaƙan Boko Haram 973 sai kuma 'ƴan kungiyar asiri 290.
Kazalika mutum 129 ne suka mutu daga cikin 'yan sintiri da mutum 100 daga masu fafutukar kafa ƙasar Biafra da masu fashi da makami 99 da ƴan bindiga masu satar mutane domin kuɗin fansa 88.
Sai dai rahoton bai mayar da hankali ba kan yawan fararen hula da aka kashe. Kamfanin ya ce ya mayar da hankali ne kan waɗanda rikicin ya shafa kai-tsaye waɗanda ke faɗa da jami'an tsaro.
Rahoton ya kuma ce alƙalummansa ba su shafi mutanen da aka kashe ba a harin da ya shafi na ƴan ta'adda ko ƴan bindiga.
Yawan jami'an tsaron Nijeriya
da aka kashe a shekarar 2021
985Jumullarsu
642Sojoji
322Ƴan sanda
11Civil Defence
5Kwastam
5DSS da Immigration da FRSC
Source: SB Morgen-BBC
No comments