Ralf Rangnick ya jinjina wa ‘yan wasan Manchester United da irin kokarin da suka yi, bayan da ya fara wasansa na farko da da kaf...
Ralf Rangnick ya jinjina wa ‘yan wasan Manchester United da irin kokarin da suka yi, bayan da ya fara wasansa na farko da da kafar dama, inda suka lallasa Crystal Palace 1-0.
Sabon kocin bai sauya ko da dan wasa daya daga tawagar da ta lallasa Arsenal 3-2 a tsakiyar makon da ya gabata ba a karkashin kulawar Michael Carrick.
‘Yan wasan United sun bai wa sabon kocin tukuicin wasa cikin karkasashi, kana magoya bayan sun nuna goyon baya a gare shi ta wajen jinjina.
Duk da cewa ‘yan United sun samu nakasu a wasa bayan hutun rabin lokaci, dan wasan nan dan kasar Brazil Fred, ya saka kwallo daya tilo na wasan.
Wannan ne karon farko da Manchester United ta yi wasa ba tare da an saka mata kwallo a raga ba a gida, bayan jerin wsanni marasa armashi a ‘yan makonnin baya a karkashin tsohon koci Ole Gunnar Solskjaer, wanda kungiyar ta sallama a makon da ya gabata.
No comments