Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

Rasuwar Ƙanin Kwankwaso Ta Shafi Duk Mutanen Kano, In ji Ganduje

Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya baiyana cewa rasuwar Kwamared Inuwa Musa Kwankwaso, ƙani ga tsohon gwamnan Kano, S...

Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya baiyana cewa rasuwar Kwamared Inuwa Musa Kwankwaso, ƙani ga tsohon gwamnan Kano, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso, ta shafi duk mutanen jihar.

A jiya Litinin ne dai Kwamared Inuwa ya riga mu gidan gaskiya, bayan ya sha jiyya a asibitin Malam Aminu Kano, inda a ka binne shi a garin Madobi.

A saƙon ta'aziya da ya fitar ta hannun Kwamishinan Yaɗa Labarai na Kano, Malam Muhammad Garba, Ganduje ya ce rasuwar marigayin, wanda ƙwararren injiniyan noma ne, rashi ne ga ɗaukacin al'ummar Kano da ma ƙasa baki ɗaya.

"Marigayi Kwankwaso ƙwararren ma'aikacin gwamnati ne kafin ya yi ritaya, musamman lokacin da ya jagoranci shirin gandun daji shekaru da dama," inji Ganduje.

Ganduje ya ce rasuwar Kwamared Inuwa ba danginsa kaɗai ta shafa ba, ta shafi gaba ɗaya Nijeriya.

Da ga ƙarshe gwamnan ya yi addu'ar Allah Ya jikan mamacin sannan ya baiwa iyali da danginsa dangana.

No comments