*Cututtuka 11 Da Shaikh Zakzaky Da Matarsa Ke Dauke Da Su Sakamakon Harbinsu Daga Ammar M. Rajab Dr Abubakar Yahaya, daya ...
*Cututtuka 11 Da Shaikh Zakzaky Da Matarsa Ke Dauke Da Su Sakamakon Harbinsu
Daga Ammar M. Rajab
Dr Abubakar Yahaya, daya daga cikin likitocin jagoran Harkar Musulunci, Shaikh Ibraheem Zakzaky da mai dakinsa Malama Zeenah Ibrahim ya bayyana kalaman babban lauyan gwamnatin tarayya (AGF) kuma ministan shari'a Abubakar Malami akan yanayin lafiyarsu a matsayin rashin gaskiya da karya tsagwaronta.
Dakta Yahaya ya bayyana hakan ne a ranar Litinin, a cikin wata sanarwa da aka aikowa da MADOGARA a Abuja mai taken: “Rike Fasfo din Shaikh Zakzaky, Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya, na da hannu a ciki.”
Ya ce da rahoton kafar yada labarai ta ruwaito Malami na cewa a ranar 22 ga watan Nuwamba, 2021, cewa yanayin rashin lafiyar ma’auratan da aka ce yana da hatsari ga rayuwarsu, ba gaskiya bane. A cewarsa, wadannan maganganun karairayi ne da Malami ya fada wanda ya yi hakan ne saboda Abubakar Malami yana son lullube laifuffukansu da dama.
“ina rubuto wannan ne a madadin Shaikh Ibraheem Zakzaky da matarsa
Malama Zeenah Ibraheem domin na daidaita lamarin. Sabanin abin da Malami ya
yi ikirari, haƙiƙa akwai sabbin shaidun da ke tabbatar da cewa dukansu su biyun
suna fama da matsalolin rashin lafiya da dama da ke da matuƙar hadari, kamar
yadda sakamakon gwaje-gwajen da suka yi na likitanci wanda aka saba gudanar na
yau da kullum ya nuna tun 2018 (bayan Shehin Malamin ya samu bugun jini na
farko, wanda a karshe hukumar DSS ta ba da damar samun Likitocinsu a karon
farko), sannan abin ya ci gaba har zuwa shekarar 2020 da 2021.
"Muna
da takardun da suke tabbatar da abin da muka fada. “Gwajin da aka gudanar a
shekarar 2019 ba wai kawai zargi bane ko karin gishiri, a’a a zahiri ma cibiyoyin
kiwon lafiya ne na gwamnati da aka amince da su suka gudanar da gwajin, wanda
ke nuni da cewa mutanen biyu na fama da cututtukan da a yanayinsu a yanzu yana
da bukatar kulawar gaggauwa kuma barazana ne ga rayuwarsu, kamar yadda kwararrun
likitocin suka tabbatar daga ciki da wajen Nijeriya - ciki har da wadanda
hukumar DSS ta gabatar.
“a bisa gaskiya, rahotan
gwajin da likitoci suka yi musu na baya-bayan nan (24 ga Satumba, 2021) an jera
cututtuka masu yawa har guda goma sha daya waÉ—anda har yanzu Shaikh Zakzaky ke
fama da su, wato: “Ciwon zuciya, girma da tabewar tsokar zuciya da ke harba
jini zuwa sassan jiki (wanda hakan ke rage aikin ta), fashewar jijiyar
kwakwalwa a sashen ‘thalamus’ hagu da dama (wanda ke haifar da shanyewar rabin
jiki), qanqancewar kofofin kashin baya (inda lakka ta shiga) na sashen wuya da
ciki, wanda ke haifar da matsanancin ciwo; rashin idon bangaren hagu, yanar ido
mai hayayyafa ta bangaren idon dama; girma da hayayyafar ‘prostate’ (wanda zai
iya haifar da ciwon sanqara/daji); gubar dalma da ‘cadmium’ mai tsanani, rauni
ga tsokokin jiki da sauran sassa masu taushi, karafa a sassan jiki daga harbin
da aka yi masa (gutsitstsiran alburushi sun kai 55 har yanzu ba a cire ba daga
jikin Shaikh) a qoqon kai, kurmin ido, tsintsiyar hannun hagu da kuma gefen
cinya; sai kuma matsalar rashin daidaiton kitse”.
“Matarsa
Malama Zeenah a rahoton gwajin likitoci na baya-bayan nan da aka yi mata (24 ga
watan Satumban 2021, gwajin ya nuna tana fama da haduwar cututtuka guda goma
sha daya da suma suke da matukar hatsari; cututtukan sune: ciwon hawan jini mai
tsanani wanda magani ya kasa sakko da shi, rugurgujewar kashin gwiwa mai
tsanani- na duka kafa biyu (wanda ya haddasa ta koma amfani da kujerar turawa
tsawon shekaru 4 yanzu) wanda kuma yana buqatar a yi tiyata a sake qoqon gwiwar
baki daya, ciwukan tsokoki da sauran sassan jiki masu taushi daga harbin
alburushi, yawaitar ciwon ciki mai tsanani wanda ke da alaqa da harbin da aka
yi mata (baqin alburusai a cikin ta); ‘gastritis (inflammation na ciki);
kumburin hanta wanda ba a san dalilin da ya kawo shi ba; sanqarar mahaifa marar
tsanani; matsalar kashin bayan ido na bangaren hagu (ya kamu da kwayar cuta);
matsalar rashin daidaiton kitse; bayyanar qullutu a mama (nonon) ta na bangaren
dama da kuma kumburin ‘lymph node’ da ke kusa da maman (ana tsoron kamuwa da
sankarar mama); da kuma taruwar ruwa a kodar ta ta bangaren dama”.
Ya ce
kwararre a fannin kiwon lafiya da hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta kawo shima
ya tabbatar da wasu cututukan da ma’auratan ke fama da su da ake danganta su da
karafa masu nauyi.
"a
don haka abin damuwa ne da rashin mutuntawa a ce hukumomin da abin ya shafa har
yanzu suna tilasta wa mutanen biyu su ci gaba da zama a Nijeriya, inda babu
wani cikakken kulawa na magani a asibitin (Nijeriya) game da irin wadannan guba
(dake jikinsu) da dukkanin cututtukan da aka lissafa," in ji shi. Yahaya
ya bayyana cewa hukumar DSS da kotu da sauran hukumomin da abin ya shafa suna
sane da tabarbarewar rashin lafiyarsu.
“A
gaskiya saboda sakamakon binciken da likitoci suka yi a shekarar 2019 ne ya sa
a karshe babbar kotun Kaduna ta bayar da umarnin a kai dukkansu asibiti domin
yi musu aikin tiyata da magani yadda ya kamata.
“Tawagar kwararrun likitocin da suka hada da
wadanda DSS da gwamnatin jihar Kaduna suka aiko a lokacin, sun tabbatar da cewa
Shaikh da matarsa suna da munanan cututtuka har guda 8 da kuma cututtuka 6
masu hatsarin gaske a lokaci guda.
“Har ila yau, a bisa gaskiya kuma kokarin da
aka yi na yi musu magani a Indiya an (gwamnati ta) hargitsa shirin baki daya
kuma jami’an tsaron da suka yi tafiya tare da su ne suka dawo da su Nijeriya.
“Tun da suka dawo daga Indiya, babu wani abu
daga cikin abubuwan da ake da bukata da aka yi wa Shehin Malamin ko matarsa,
kuma har yau ana nan a hakan.
"Duk
da kokarin da likitocinsu suke yi, yanayin lafiyarsu dangane da wadannan
cututtukan na kara tabarbarewa, a sakamakon haka har yanzu suna bukatar
gaggawar samun wadannan magunguna a wajen Nijeriya, kamar yadda aka saba kuma
har yanzu masana ne ke ba da wannan shawarar," in ji shi.
A
cewarsa, sabanin ikirari na karya da Abubakar Malami ya yi na cewa babu daya
daga cikin likitocin su da ya yi wani gwaji, musamman likitocin biyu da aka
ambata, a zahiri an gudanar da gwaje-gwajen ne ta hanyar dakunan gwaje-gwajen
asibiti da gwamnati ta amince da su, wanda ya nuna sabon binciken da aka samu a
Asibitin Malam Aminu Kano da Asibitin koyarwa na Barau Dikko (AKTH/ Barau Dikko
Teaching Hospital a shekerar 2020 da kuma Synlab Abuja a shekarar 2021),
sakamakon bai sauya ba ko daya daga cikin abin da aka bukata na kulawar
asibiti/tiyata waÉ—anda aka bayar da shawara ga dukkansu tun a cikin shekarar
2019.
Ya
bayyana cewa, duk kokarin da ake yi kan Zakzaky da matarsa a baya-bayan nan na
magani abin ya ci tura ya zuwa yanzu sakamakon rashin fasfo na kasashen waje.
“samar
da takardun tafiye-tafiye da sauran dukkanin abin da ake da bukata a kasashe da
ake sa ran za a yi musu tiyata da sauran kulawar lafiya, bisa shawarwarin da
dukkanin kwararru likitoci da suka yi nazari akan matsalarsu ya zuwa yanzu.
“A
gaskiya ma, ikirarin da Malami ya yi na cewa babu bukatar gaggawa ga ma’auratan
na zuwa kasar waje domin duba lafiyarsu ya kara tabbatar da cewa yana da hannu
wajen hana su fasfo da sake ba su wasu sabbi.
“Ya
kamata wakilin tsokanar ya lura da cewa ko da ko babu rashin lafiyar, Shaikh
Zakzaky da matarsa suna da ‘yancin mallakar fasfo na Nijeriya da kuma tafiya
duk inda suke so.
“Yana daga cikin hakkokinsu, sai dai idan Abubakar Malami doka ne
shi a kashin kansa," in ji Yahaya.
No comments