Bangaren Jam’iyyar APC a Jihar Legas da ake yi wa lakabi da ‘Lagos-4-Lagos’ ya bayyana matakinsu na komawa Jam’iyyar PDP a wani ...
Bangaren Jam’iyyar APC a Jihar Legas da ake yi wa lakabi da ‘Lagos-4-Lagos’ ya bayyana matakinsu na komawa Jam’iyyar PDP a wani biki da aka gudanar wanda ya samu halartar tsohon shugaban Majalisar Dattawan kasar Bukola Saraki.
Bangaren Jam’iyyar APC dake karkashin Olajide Adediran ya dade yana takun saka da shugabancin Jam’iyyar a matakin jiha da kuma Tarayya, abin da ya kai ga gudanar da tarurrukan jam’iyyar guda biyu a matakan Unguwanni da kananan hukumomi da kuma jiha.
Sai dai Jam’iyyar APC ta kasa ta ki amincewa da taron da bangaren Adediran ya gudanar, inda ta amince da na bangaren jagoran Jam’iyyar na sa Bola Ahmed Tinubu da Gwamna Babajide Sanwo-Olu.
Rfi ta labarto cewa; jagoran bangaren da ya sauya shekarar Adediran ya gabatar da korafe korafe da dama da ya ce sun mamaye Jam’iyyar ta su ta APC da suka hada da kama karya da kuma hana 'ya'yan jam’iyyar bayyana ra’ayoyin su a lokacin da ya dace.
Rahotanni sun ce Adediran na shirin tsayawa takarar gwamna a zaben shekarar 2023 domin kalubalantar Jam’iyyar APC da jagororinta a jihar, abin da ya sa ya sauya sheka tare da magoya bayansa daga kananan hukumomi 20 na Jihar Legas.
Tsohon shugaban majalisar Dattawa Bukola Sarki ya yi maraba da sabbin ‘ya'yan jam’iyyar, inda ya shaida musu cewar sun koma jam’iyyar dake shirin ceto Nijeriya daga ukubar da APC ta jefa Jihar Legas da kuma kasa baki daya.
Jihar Legas na daya daga cikin jihohin Nijeriya da Jam’iyyar APC ke fuskantar rikicin cikin gida sakamakon rarrabuwar kawunan da aka samu wajen gudanar da tarurrukan zaben shugabannin jihohi.
No comments