Ronaldo Zai Bayar Da Mamaki A Karkashin Sabon Kocin Man United -Carrick


Michael Carrick ya yi amannar cewa babu abin da zai hana Cristiano Ronaldo yin rawar gaban hantsi a salon wasan sabon kocin wucin gadi na Manchester United, Ralf Rangnick.

Ana ta rade radin cewa Ronaldo zai gaza tabuka wani abu a salon wasan Rangnick mai kama da na ‘yada kanin wani.

United ta dauki Rangnick a matsayin kocin wucin gadi har zuwa karshen wannan kaka bayan da ta sallami kocinta, Ole Gunnar Solskjaer. 

Post a Comment

0 Comments