Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

Saboda Omicron Saudiya Ta Haramtawa 'Yan Nijeriya Shiga Kasar Ta

Gwamnatin Saudi Arebiya ta bi sahun wasu kasashen duniya wajen hana jiragen sama da suka tashi daga Nijeriya shiga kasar sakamak...


Gwamnatin Saudi Arebiya ta bi sahun wasu kasashen duniya wajen hana jiragen sama da suka tashi daga Nijeriya shiga kasar sakamakon samun wasu mutanen dake dauke da sabon nau’in cutar korona da ake kira Omicron.

Wannan mataki na zuwa ne kwana biyu bayan Birtaniya da Canada sun haramtawa baki daga Nijeriya shiga kasar su sakamakon samun masu dauke da cutar.

Rahotanni daga birnin Kano sun ce yanzu haka maniyyata Umrah da dama sun makale a birnin sakamakon wannan mataki da Saudiyar ta dauka, yayin da jami’an kula da tashohin jiragen saman Malam Aminu Kano suka tabbatar da samun umurnin hana jirage tashi zuwa kasar.

Wata matafiya da yanzu haka take birnin Kano akan hanyar ta na zuwa Umrah a kasar ta Saudiya ta shaidawa RFI Hausa cewar tabbas an sanar da su cewar gwamnatin Saudiya ta soke tafiyar su daga Nijeriya.

Jaridar Daily Trust ta jiyo ta bakin wani jami’in ofishin Jakadancin Saudiyar dake Kano na cewar tabbas sun samu umurnin hana jiragen sama daga Nijeriya tafiya kasar.

Sai dai Jaridar ta ruwaito cewar duk da wannan umurnin, wani babban jami’in kamfanin jiragen sama ya shaida mata cewar jirage biyu sun tashi yau da safe daga Abuja zuwa Jeddah wadanda suka hada da Qatar Air da Badar Air.

Gwamnatin Nijeriya ta bakin ministan yada labarai Lai Mohammed ta bayyana bacin ran ta da irin wannan mataki da kasar Birtaniya da kuma Canada suka dauka na hana baki daga Nijeriya zuwa kasar.


No comments