Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

Sarkin Kano, Aminu Ado Zai Kara Aure Da Sahibarsa Da Suka Dade Suna Soyayya

Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero na shirin angwancewa da sahibarsa da su ka daɗe su na soyayya, wacce a ke kiranta da Hajiya...Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero na shirin angwancewa da sahibarsa da su ka daɗe su na soyayya, wacce a ke kiranta da Hajiyayye, da ke Unguwar Ɗorayi a Jihar Kano kamar yadda Jaridar Daily Nigerian ta labarto.

Sarki Bayero, wanda matar shi ɗaya da ƴaƴa huɗu, zai ƙara aure bayan ya shafe kusan shekaru talatin da mata ɗaya.

Wata majiya ta shaidawa jaridar DAILY NIGERIAN cewa shirye-shirye sun nisa tsakanin waliyyan Sarkin da kuma na amaryar.

Majiyar ta ƙara da cewa ba za a yi wani gagarumin biki ba sabo da "Mai martaba ba mutum ne mai son fankama ba", kuma itama amaryar dangin ta ba sanannu ba ne.

"Nan ba da daɗewa ba za a yi bikin. A baya dai an ɗaɗɗaga bikin, amma da yanke ba wani gagarumin biki za anyi ba, to da ga yanzu, ko da yaushe ma za a iya yin auren.

"Sarkin ya daɗe su na soyayya da Hajiyayye kafin ma ya zama Sarki. Amma yanzu dai an kammala shirye-shirye na bikin," in ji majiyar.

An haifi Sarki Aminu Ado Bayero a shekarar 1961, in da a ranar 9 ga watan Maris ya zama Sarki na 15 na kabilar Fulani, bayan da Gwamna Abdullahi Ganduje tsige ɗan yayansa, Sarki Sanusi. 

No comments