Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Sarkin Shaidanu Ya Mutu A Nijeriya

Wani  boka a Nijeriya da ake yi wa lakabi da Sarkin Shaidanu wanda kuma ke  da ‘ya’ya da jikoki sama da 300 da mata 59, Simon Od...


Wani  boka a Nijeriya da ake yi wa lakabi da Sarkin Shaidanu wanda kuma ke  da ‘ya’ya da jikoki sama da 300 da mata 59, Simon Odo ya mutu. 

Mista Odo wanda haifaffen garin Aji ne da ke karamar Hukumar Igbo-Eze a jihar Enugu, ya mutu ne a sanyin safiyar ranar Talata bayan fama da gajeruwar jinya.

Daya daga cikin ‘ya’yansa, Emeka Odo ya tabbatar da mutuwar mahaifinsu ga Kamfanin Dillancin Labarai na NAN, yana mai cewa mahaifin nasu ya mutu ne yana da shekaru 74.

Tuni aka fara shirye-shiryen yi masa jana’iza daidai da wasiyar da marigayin ya bar wa iyalansa, inda ya ce musu kar su kuskura su ajiye gawarsa a dakin ajiyar gawarwaki.

Sarkin Shaidanun ya ce, lallai a yi gaggawar yi masa jana’iza jim kadan da rasuwarsa kamar yadda Mista Emeka ya bayyana.

No comments