Sergio Aguero ya sanar da yin ritaya daga ƙwallon ƙafa ƙasa da wata shida da ya koma taka leda a Barcelona. Aguero ya ce ya yi ritaya ne s...
Sergio Aguero ya sanar da yin ritaya daga ƙwallon ƙafa ƙasa da wata shida da ya koma taka leda a Barcelona.
Aguero ya ce ya yi ritaya ne saboda kare lafiyarsa.
Ɗan wasan wanda ya fi yawan cin ƙwallo a Manchester City ya ce yana alfahari da rayuwarsa ta ƙwallon ƙafa tare da amincewa da makomarsa da ya kira mafi ƙalubale.
A ranar 30 ga Oktoba aka tafi da ɗan wasan asibiti bayan fama da ciwon ƙirji a lokacin da Barcelona ta yi 1-1 da Alaves.
No comments