Shekarar 2022 Shekara Ce Ta Sulhu Da Zaman Lafiya -Ganduje



Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya ce ya kamata sabuwar shekara ta 2022 ta kawo sabon zaman lafiya da sulhu a tsakanin masu ruwa da tsaki a jam’iyyun siyasa a jihar da ma Æ™asa baki É—aya.

Gwamnan ya ce ya kamata a ce watanni masu zuwa su zama na siyasar cikin gida, inda za a  samu ci gaba a jam’iyyun siyasar jihar, inda ya Æ™ara da cewa yin hakan zai samar da wakilai masu nagarta a matakai daban-daban wadanda su ke da Æ™warewar da za su ci gaba da gina Kano kan tsare-tsare da manufofin da shugabannin da su ka shuÉ—e su ka assasa.

 A saÆ™on sabuwar shekara ga al’ummar jihar, wanda Kwamishinan YaÉ—a Labarai na jihar, Malam Muhammad Garba ya fitar, gwamnan ya ce da ga dukkan alamu abubuwan da su ka faru a Kano na iya kawo wani sabon salo a tarihin siyasar jihar.

 Ya ce al’ummar Kano da ke da kishin cigaban jihar sun nuna buÆ™atar ganin manyan Æ´an siyasar jihar sun yi sulhu da juna, domin ganin an samar da zaman lafiya da ci gaba mai inganci a fagen siyasa da al’amuran cigaban al’umma.

 Sanarwar ta nuna matuÆ™ar damuwa kan yadda ake ta fama da taÉ“arÉ“arewar tsaro a faÉ—in Æ™asar, baya ga fatara da a ke fama da ita sakamakon taÉ“arÉ“arewar tattalin arziki a Æ™asa.

 Sai dai ya bayyana fatansa na cewa duk da Æ™alubalen da a ke fuskanta,  gwamnatin Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari na ci gaba da Æ™oÆ™arin ganin an aiwatar da manufofinta da shirye-shiryen yadda za a ragewa al’umma radadin talauci.

 Gwamnan ya kuma ba da tabbacin cewa gwamnatin sa, wacce kasafin kuÉ—in 2022 ya maida hankali wajen kammala aiyuka, da Æ™udurin aniyar kyautata wa al’umma ta hanyar kawo sauyi a yankunan karkara da kuma shirye-shiryen karfafa tattalin arzikin Jihar Kano.

 Yayin da yake taya al’ummar kasar murnar shigows sabuwar shekara, Ganduje ya kuma yi kira da a hada kai da yi wa Najeriya addu’a musamman malaman addini su rika wa’azi akan zaman lafiya, hakuri da juna duk da kalubalen da ake fuskanta.

Post a Comment

0 Comments