Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

SHEKARU 6 DA KISAN KIYASHIN SOJOJI A ZARIYA: Mabiya Harkar Musulunci Sun Gudanar Da Taron Tunawa A Abuja

Daga Ammar M. Rajab Kamar yadda suka saba a duk shekara suna gudanar da taron tunawa da kisan da kiyashin da sojojin Nijeriya su...


Daga Ammar M. Rajab

Kamar yadda suka saba a duk shekara suna gudanar da taron tunawa da kisan da kiyashin da sojojin Nijeriya suka aikata akan ‘yan’uwa Musulmi almajiran Shaikh Ibraheem Zakzaky a ranekun 12 zuwa 14 ga watan Disambar 2015, a bana ma ba su yi kasa a guiwa ba, a inda da safiyar ranar Lahadin 12 ga watan Disambar 2021 suka gudanar da gagarumin taron tunawa da kisan kiyashin sojojin a dakin taro na Yesmin Event Centre dake garin Gwagwalada a Birnin Tarayya Abuja.

Wakilinmu da ya halarci taron ya labarto mana cewa Farfesa Isa Hasan Mshelgaru, daga Jami’ar Ahmadu Bello dake Zariya, shi ne mai jawabi na farko a taron, inda ya yi jawabi kan hujjoji da adadin mata da kananan yara da sojoji suka yi wa kisan kiyashi a Zariya.

Malama Ruhi Rizvi daga kasar Birtaniya ta kasance mai jawabi na biyu, inda ta yi jawabi kan nazarin martanin kasashen duniya kan kisan kiyashin Zariya wanda aka haskta ta hanyar majigi.

Mai jawabi na uku a taron shi ne; mai rajin kare hakkin bil’adama, kuma shugaban kungiyar ‘Concerned Nigerians’, Prince Deji Adeyanju, ya yi jawabi a kan maudu’i mai taken matakan tunkarar take hakkin dan Adam. Shima an haska ne ta hanyar majigi.

Jagoran Harkar Musulunci, Shaikh Ibraheem Zakzaky ne ya gabatar da jawabin rufe taron, wanda aka haska ta hanyar majigi ga mahalarta taron.

Dukkanin jawaban an gudanar da su ne a harshen Turanci. Kuma taron ya samu halartar dimbin ‘yan’uwa maza da mata, yara da kanana daga sassa daban-daban na kasarnan.

A karshe bayan kammalawa an rufe taro da addu'a wanda Shaikh Sanusi Abdulkadir ya gabatar. 

Sannan an gudanar da 'exhibition' dangane da kisan kiyashin sojojin a Zariya, sannan aka sallami al'umma. 

Dandalin Academic Forum, Sisters Forum da kuma Mu’assatus Abdul Fadl Abbas ne suka shirya taron a madadin Harkar Musulunci a Nijeriya.

Tunda fari an fara taron ne da bude shi  da addu’a, karatun Alkur’ani mai girma, an gudanar da Display daga Kashshaful Imam Mahdi da Intizar da sauran su. An kuma gudanar da wakokin juyayin kisan kiyashin sojojin wanda Shamsu Fudiyya da Alhaji Mustapha Gadon Kaya suka yi a lokuta daban-daban.


No comments