Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya isa Saudiyya a jiya Asabar, inda ya zama shugaban manyan kasashen yammacin duniya na farko d...
Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya isa Saudiyya a jiya Asabar, inda ya zama shugaban manyan kasashen yammacin duniya na farko da ya ziyarci kasar tun bayan kisan gillar da aka yi wa dan jaridar Saudiyya kuma marubucin jaridar Washington Post, Jamal Khashoggi a shekarar 2018.
Macron zai gana da mai jiran gadon Masarautar Mohammed bin Salman a wani bangare na rangadin da yake yi a yankin Gulf.
Kasashen biyu za su tattauna batutuwan da suka shafi yankin da suka hada da rikicin kasar Lebanon da kuma dakatar da tattaunawar nukiliya da Iran.
Kisan Khashoggi ya janyo cece-ku-ce a tsakanin kasashen duniya da ke ci gaba da tada jijiyoyin wuya. To sai dai shugaba Macron na cewa babu yadda za a yi hulda na kasashen yankin tare da watsi da Saudiyya da ta fi karfi a yankin.
(RFI)
No comments