Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

Sojojin Nijeriya Sun Yi Nasarar Kakkabe Mayakan Bello Turji A Sakkwato

'Yan bindiga da dama daga cikin ‘ya'yan kungiyar Bello Turji aka bayyana cewar sun mutu a Jihar Sakkwato sakamakon bude ...

'Yan bindiga da dama daga cikin ‘ya'yan kungiyar Bello Turji aka bayyana cewar sun mutu a Jihar Sakkwato sakamakon bude wutar da sojojin kasar suka musu a kauyen Katanga dake karamar hukumar Isa.

Shaidun gani da ido sun ce babban kwamandan sojin dake kula da runduna ta 8 Manjo Janar Uwem Bassey ya jagoranci tawagar sojoji tare da manyan jami’an sa a cikin motocin yaki sama da 20, wadanda suka yiwa ‘Yan bindigar kofar rago, yayin da sojin sama suka taimaka musu da ruwan wuta ta sama.

Bayanan dake zuwa daga ‘Yankin sun ce sojojin sun yi nasarar kashe ‘Yan bindigar da dama tare da kona matsugunin su, yayin da suka ci gaba da bin sawun wadanda suka tsere daga kauyen domin kaucewa ruwan wutar. 

Janar Bassey ya sha alwashin murkushe wadannan ‘Yan ta’addan da suka hana zaman lafiya a yankin tunda ya karbi ragamar jagorancin rundunar samar da zaman lafiya ta ‘Operation Safe Haven’, kuma rahotanni sun tabbatar da cewar da kan sa yake jagorancin sojojin dake kai harin cikin dazukan jihar.

Jihar Sakkwato na daya daga cikin Jihohin Arewa maso Yammacin Nijeriya da ‘Yan bindiga suka mamaye wasu sassan ta, inda suke kai munanan hare hare suna hallaka jama’a.

Makwanni biyu da suka gabata, ‘Yan bindigar sun kai kazamin hari karamar hukumar Sabon Birni inda suka kona wasu matafiya sama da 40 a cikin motar su, abin da ya sake tada hankalin jama’ar Nijeriya baki daya.

Wannan ya sa gwamnan jihar Aminu Waziri Tambuwal ya ziyarci shugaban kasa Muhammadu Buhari inda ya bukaci kafa dokar ta baci a wasu yankunan jihar domin dakile ayyukan wadannan ‘Yan bindiga.

Kafin ziyarar, Gwamnan ya gabatar da korafi akan yadda sojojin suka gudanar da shirin kakkabe ‘Yan bindiga a Jihar Zamfara ba tare da tsara yadda zasu kare masu tserewa daga yankin suna fada wasu jihohi ba.

Tambuwal yace wasu daga cikin wadanda aka tarwatsa a Jihar Zamfara yanzu haka sun kutsa kai cikin jihohin dake makotaka da su, ciki harda Sokoto inda suke kai munanan hare hare akan fararen hula.


No comments