Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

Tafiyar Shaikh Zakzaky Zuwa Indiya: Gaskiyar abin da ya faru -Daga Zeenah Ibraheem

Fassarar Ammar M. Rajab  Na yanke shawarar tallata wannan rubutun ne a yanzu, domin an ja hankalina ga wani ikirari mai cike da ...


Fassarar Ammar M. Rajab 

Na yanke shawarar tallata wannan rubutun ne a yanzu, domin an ja hankalina ga wani ikirari mai cike da kura-kurai da babban mai shari’a, Malami Abubakar ya yi a kwanan nan a wata sanarwar manema labarai kan tafiyar takaicin da muka yi zuwa Indiya a watan Agustan 2019.

Bayan umarnin kotu da kuma amincewar da shugaban kasa ya bayar kan Shaikh Zakzaky (H) da ni kaina akan mu nemi magani a Indiya amma a karkashin abin da Alkalin ya kira da "tsattsauran kulawa" daga gwamnati, Hukumar tsaron farin kaya, jami'an DSS sun gayyaci iyalinmu domin tattaunawa game da tsarin yadda za a aiwatar da umarnin kotu.

Amma abin ya bai wa iyalinmu mamaki, zaman ba zaman tattaunawa ba ne ko kadan. A maimakon haka, wani mutum da aka gabatar da shi a matsayin wakilin hukumar leken asiri ta Nijeriya (NIA) – hukumar da aka kirkira daga hukumar CIA ta Amurka - ya yi jawabi ga tawagar, inda ya shaida musu cewa gwamnati na shirin sauya asibitin a Indiya daga MEDANTA MEDICITY zuwa wani asibiti mai suna FORTIS HOSPITAL.

Na biyu, ya kuma sanar da su cewa gwamnati ta samu jirgin sama mai zaman kansa mai daukar fasinjoji 12 da ke shirin jigilar Shaikh da wadanda za su raka shi. Ya ce shida daga cikinsu jami’an tsaro ne. 2 daga DSS, 3 daga NIA da kuma 1 Likitan ‘yan sanda. Ya ci gaba da cewa mutane 3 kawai za su bari su raka mu.

Bisa wadannan dankarawa, Muhammad danmu, wanda yana daga cikin iyalinmu da suka halarci zaman ya ki amincewa da hakan. Ya tunatar da jami’an tsaron cewa kotu ta bayyana filla-filla cewa gwamnati za ta sa ido kawai ne ba wai ta yanke hukunci ko daukar nauyin tafiyar ba. A bisa wannan dalilin ya ki amincewa da ra’ayin gwamnati na samar da jirgin sama mai zaman kansa ko sauya asibiti ko kuma ta takaita adadin wadanda za su raka mu. Ya kuma sanar da jami’an tsaro wani shiri a bangarensu na samar da jirgin sama domin tafiyar.

Wannan din, jami'an tsaron suka yi watsi da hakan. Muhammad kuma ya ki amincewa da yin tafiya tare da wannan Likitan 'yan sandan saboda akwai tantama a kansa. Tuntuni dama Shaikh din ya ki amincewa da kulawar likitocin gwamnati tun bayan da ya samu hawan jini na farko a watan Janairun 2017.

Bayan doguwar tattaunawa da jami'an tsaron tare da tuntubar Shaikh daga karshe, an cimma matsaya kan irin jirgin da za a yi amfani da shi wajen tafiyar. An amince cewa Shaikh, da Ni da wadanda za su raka mu su sayi tikitin jirginmu su sanar da gwamnati, domin ita ma gwamnati ta sayi tikitin jami’an tsaron da za su raka Shaikh da ni kaina.

Kuma tunda jami’an tsaron ne suka samo wa kowa biza, sai suka tsaya tsayin daka wajen samar da biza ga mutane 3 kawai da za su raka mu. Wanda ya hada da likitan gida, da kuma mutum biyu.

Har ya zuwa lokacin da muka tashi daga filin sauka da tashi na jirgin sama na Abuja, gwamnati ta nace kan matsayarta na sauya asibitin da za mu je a Indiya. Hasali ma, a lokacin da muke filin sauka da tashi na jirgin sama na Abuja, mun samu labarin cewa asibitin Medanta na fuskantar matsin lamba da barazana daga gwamnatin Amurka a kan ka da su sake su karbe mu. A bisa wannan, sun sanar da likitocinmu cewa ba za su karbe mu a asibitin ba.

Amma da muka isa Dubai, mun samu labarin cewa a yanzu, asibitin Medanta ya amince zai karbe mu.

Mun sauka a Indiya a ranar Talatar 13 ga watan Agustan 2019 kuma an karbe mu a filin jirgin sama daga abin da ya bayyana cewa tawagar likitoci ne, ma'aikatan jinya, da kuma masu fatan alheri. Likitocin da ma’aikatan jinyar na sanye da kayan aiki wanda tambarin asibitin Medanta ya bayyana tangaran.

Nan da nan "Likitocin" suka dora Shaikh akan gadon motar dake daukar marasa lafiya suka dauke shi tare da ni. Wannan karamcin abin mamaki ne domin ba su da bukatar su yi haka. Tunda zai iya zama da kanshi.

Amma a kan hanyar zuwa asibiti, wani “Likita” wanda ya yi ikirarin shi Shi’a ne, wanda kuma ya yi ikirarin cewa sunansa Ali Ridha ya shaida wa Shaikh, da ni kaina da kuma likitanmu na gida cewa a gaskiya sun yaudari dimbin jama’a masu fatan alheri da suka taru a filin jirgin domin tarbar Shaikh din ta hanyar ajiye motocin daukar marasa lafiya guda biyu a kofar shiga (filin jirgin) daidai inda suka taru su kuma suka fita da mu ta wata kofar.

Abin da ya ba mu mamaki da kuma wadanda suka raka mu shi ne, babu daya daga cikin likitocin da suka zo “Nijeriya” daga Indiya cikin wadanda suka same mu a filin jirgin sama.

Da isar mu asibitin, “likitan” nan dai wanda ya yi ikirarin cewa sunansa Ali Ridha shi ne dai ya sake shaida mana cewa za su yi amfani da kofar baya na asibitin domin gujewa wadansu taron jama’a masu fatan alheri da suka taru a asibitin.

Bayan isa kusa da asibitin, akwai ‘yan sanda dauke da makamai a ko’ina da kuma wasu da suka yi kama da jami’an tsaro da oba-oba (walkie-talkie) a hannunsu! Wadannan dukkansu ‘yan “Nijeriya” ne da jami’an tsaron Indiya. Haka kuma akwai jami'ai daga ofishin jakadancin “Nijeriya” da ke Indiya.

Nan da nan aka kai mu sashen gaggawa da kulawa. Sai bakin "Likitoci" suka fara tambayar Shaikh da ni kaina. A bayyane yake ba su san komai dangane da yanayin rashin lafiyarmu ba. Nan take suka kawo kayan asibiti suna rokon Shaikh da ni kaina a kan mu sanya su ba tare da la'akari da ladubban shari’ar Musulunci a kaina ba. Haka kuma sun kawo alluran da suka yi ikirarin cewa allurar tramadol ce da wasu kwalabe domin daukar samfurin jini.

Dukkanin matsalar ta fara ne a lokacin da Shaikh din ya bukaci ya ga amintattun likitocinsa kafin a yi komai. Sai suka zama masu adawa da hakan har ma da nuna iko, suna cewa babu wani Likita daga wajen asibitin da za a bari ya shiga cikin kulawar lafiyar Shaikh da ni kaina.

Ganin irin wannan yanayi na rashin tausayi, da kuma yadda muka yi tafiya mai nisa, tare da la’akari da jikin marasa lafiya da ya gaji, Shaikh din ya nemi a bar shi ya samu masauki a otal domin ya huta har zuwa washegari, saboda ya tuntubi amintattun likitocinsa domin daukar matakin da ya dace a cikin wannan yanayin. Amma aka yi watsi da wannan bukatar cikin rashin kunya. Bilhasalima wani dan sanda ya zo ya dakawa Shaikh tsawa cikin rashin kunya, yana gaya masa cewa, ko dai ya mika kansa domin a yi masa magani daga wadancan Likitocin ko kuma ya koma “Nijeriya”!

A daidai wannan matakin, wani jami’in ofishin jakadanci ya shaida wa Shaikh cewa kafin ya iso kasar Indiya, jami’an ofishin jakadancin sun yi wata ganawa da jami’an tsaron Indiya da kuma mahukunta asibitin a kan yadda za a yi wa Shaikh da ni kaina magani. Kuma ya sanar da Shaikh cewa kawai ya mika wuya ga abin da suka amince da shi kuma ba shi da ta cewa yadda Likitoci za su yi masa. Ya kuma ce wadancan "Likitocin" na Medanta ne za su duba shi kuma su yanke shawarar yadda za a yi maganinsa kuma ba su damu da abin da Likitocinsa suka gano kawo yanzu ba.

A nan ne Shaikh, da ni, da wadanda suka rako mu muka fahimci cewa hakika mun fada tarkon da hadin guiwar gwamnatocin Nijeriya da Indiya suka kulla. Bilhasalima, ya zuwa ranar Larabar 14 ga watan Agusta mun gano cewa galibin wadanda suka tarbe mu a filin jirgin sama sanye da kayan Likitoci gaba dayansu ba likitoci ba ne illa jami’an tsaro da suka yi shigar likitoci.

A don haka Shaikh din ya shaida musu cewa ya amince a kwantar da shi a asibiti har sai ya samu damar tattaunawar da yakamata da likitocinsa da kuma hukumomin asibitin.

An ba mu dakuna a asibitin. Shaikh din da ni kaina a dadi daya. Ba a barinmu mu fito daga dakin mu. Jami’ai dauke da makamai suna wajen dakin kuma ba za a iya kulle dakin daga ciki ba. Kuma jami’an dauke da makamai suna shigowa dakin su fita duk yadda suka ga dama a tsawon dare harma da rana. Haka na sanya hijabi a duk tsawon zamanmu daga Talata zuwa Alhamis.

Tsarewar da aka yi mana a asibitin Medanta ya fi tsarewar da aka yi mana a “Nijeriya” tsanani.

Daga baya Shaikh din ya samu labarin cewa an bai wa asibitin bayanan karya ne. An sanya su sun yarda cewa gwamnatin Nijeriya ce ta kawo mu domin a yi mana magani.

An sanya Asibitin sun yarda cewa hukumomin Nijeriya ne suka kawo wasu masu aikata miyagun laifuka dauke da cututtukan da ba a san su ba domin a yi musu magani. Kuma wadannan masu aikata laifukan ya zama dole a kiyaye su sosai domin ka da su tsere.

Bayan da muka fahimci irin tarkon da muka fada a ciki, da kuma yanayin rashin aminci a ciki, sai ya bayyana kamar hasken rana cewa ba za mu iya amincewa wannan asibiti ba kuma. Maganar gaskiya, amincinmu ga sanannun likitocin Indiya da kuma ‘yan’uwan da suka gabatar da su ta sa Shaikh din ya amince da zuwa Indiya tun da farko. A yanzu tunda aka cire wadannan Likitocin da karfi daga kula da lafiyarmu, wannan amincin ya rushe.

Amma duk da haka, Shaikh din ya bukaci mahukumtan asibitin bayan ya tuntubi Likitocinsa da su jinkirta masa daga duk wani magani har na tsawon sa’o’i 48, har sai ya samu damar tuntubar Likitocinsa da sauran abokansa a kan matakin da ya dace ya dauka. Da farko sun amince kuma har aka sanya hannu a kan yarjejeniyar amincewar.

Amma a ranar Laraba, wannan jami’in na ofishin Jakadanci ya sake zuwa domin lallashin Shaikh din da ya bari a yi masa magani a asibitin daga wadannan bakin likitocin da ba su sani ba amma a wannan karon ya mutunta shi. Zakuwarsa da hakan ya bayyana matuka kuma abin kokwanto ne.

Kuma a kan wannan lallashin ne Shaikh din ya bukaci a ba shi damar tuntubar Sayyid Masoud Shadjarah, wanda a lokacin yana kan hanyarsa ta zuwa Indiya daga Birtaniya (U.K) da kuma Likitocinsa na Indiya da sauran abokansa domin yanke shawarar da ta dace.

Amma washegari, wanda yake ranar Alhamis din 15 ga watan Agusta ne, sai suka hana Likitocin Indiya su ga Shaikh. Kuma suka ki yarda Sayyid Masoud Shadjarah ya gana da Shaikh, duk da cewa shi da Likitoci sun yi wuni daya a wajen asibitin.

Amsar da jami’in ofishin jakadanci ya bayar washegari shi ne mu shirya domin a dawo da mu Nijeriya nan da sa’a 2 da rabi. Jirgin Habasha ne ya dawo da mu, a yayin da muka je ta jirgin Emirates.

Bayan dawowa “Nijeriya” wadansu bayanai sun rika bayyana. Ga wasu daga cikinsu:

1)      An jiwo wani dan majalisa a “Nijeriya” yana cewa; “Ya aka yi aka ji likitocin Indiya suna magana da harshen Ibrananci (Hebrew)?”

2)      Watakila, majiyarsa ta kasance daga wasu jami'an tsaron Nijeriya ne da suka kasance a wurin.

3)      Wasu sun ce wani tsararren shiri ne na kisan gilla da CIA ta shirya, tare da hadin guiwar Saudiyya domin yi wa Shaikh Zakzaky (H) irin abin da suka yi wa Khashoggi.

Sun yi shirin mayar da dukkanin zargi a kan Hukumar kare hakkin bil’adama ta Musulunci ta Landan tare da hadin guiwar asibitin MEDANTA.

*KAMMALAWA:*

Duk da yake, an fitar da wasu faifan saurare (audio) da bidiyo har guda uku na Shaikh Zakzaky (H) wanda a ciki shi da kansa ya yi bayanin a yayin da abubuwan suke faruwa, mun yi mamakin da fahimtar wasu masu kyakkyawar niyya sakamakon jahiltar gaskiyar abin da ya faru ko kuma rashin fahimta ya sa su maganganu kamar: “An san Shaikh Zakzaky mutum ne mai hakuri, me zai hana shi ya yi hakuri ya zauna a Indiya har a yi masa magani?"

Ko da yake wasu sun yi irin wadannan kalaman ne da gangar da kuma yaudara domin birkita tunanin al’umma. Amma ni ban damu da irin wadannan mutanen ba, tunda su a ko wanne irin hali, za su dora wa wanda suka tsana laifi ne. Amma na yanke shawarar yin bayani ne kawai saboda amfanar mutane masu kyakkyawar fahimta.

Yakamata ku fahimci cewa, Shaikh din ya amince ya tafi Indiya domin jinyarsa ne saboda amincewar da yake da shi ga Likitocinsa na Indiya da sauran abokansa da suka ba da shawarar zuwa Indiya. Amma da isarsa can, ofishin jakadancin Nijeriya tare da hadin gwiwar gwamnatin Indiya da kuma tabbas ofishin jakadancin Amurka suka karbe ikon komai. Kuma an gaya masa kai tsaye cewa Likitocinmu da abokanmu dole ne su yi biyayyya da matakin da wadanda na ambata a sama su uku za su yanke kuma ba za su iya wata magana ba game da jinyar mu.

Kari a kan wannan, shi da ni kaina an yi mu’amala da mu cikin tsauri da rashin kunya! Nan da nan, asibitin ya zama wani gidan yari kuma mafi muni fiye da wanda muka baro a baya! A cikin wannan yanayin, amanar da ta sanya ita ce babban dalilin da ya sa muka amince muka tafi Indiya ta rushe baki daya.

Zai zama wauta, bayan duk wadannan mu mika kanmu ga irin wannan yanayi mai hadarin gaske.

Shaikh din ya bayyana cewa a shirye yake azzalumai su kashe shi amma ba wai a fake da sunan neman magani ba. Idan har sun ga dama, suna iya barin shi ya mutu da gubar dake jikinsa, ko kuma su yi amfani da makamansu su kashe shi. Zai bayyana ga kowa da kowa cewa suna da alhakin kashe shi. Amma ba yadda za a yi ya taimake su wajen kashe shi a sirrance.

Kuma a karshe, yana da kyau kowa da kowa ya sani cewa gwamnatin Nijeriya ce ta yanke shawarar ta dawo da mu da gaggawa Nijeriya ba tare da ta ba mu damar tuntubar Likitocinmu da abokan huldar mu ba ko da yiwuwar sauya wani asibiti wanda mu da Likitocinmu ne za su kasance masu ikon kula da lafiyarmu.


DAGA ZEENAH IBRAHEEM, MATAR SHAIKH IBRAHEEM ZAKZAKY

29 GA WATAN NUWAMBAN 2021

No comments