Kungiyar Taliban ta kafa dokar haramta yi wa mata auren dole a Afghanistan, tana mai cewa bai kamata a dauki matan a matsayin ka...
Kungiyar Taliban ta kafa dokar haramta yi wa mata auren dole a Afghanistan, tana mai cewa bai kamata a dauki matan a matsayin kadara ba, a don haka dole ne su amince da zabin wanda ake shirin aura musu.
Shugaban kungiyar Taliban Hibatullah Akhunzada, ya sanar da kafa dokar hana auren dolen a ranar Juma’a.
Dokar dai ba ta ambaci adadin shekarun da za a yi wa mace aure ba, shekarun da a baya aka sanya na farawa ne daga 16.
Kungiyar ta Taliban ta kuma ce daga yanzu za a bar matar da mijinta ya rasu ta sake yin aure makwanni 17 bayan mutuwar mijinta, kazalika da kanta za ta zabi sabon mijin da take son aura.
No comments