Kungiyar kwallon kafa ta Tottenham ta fice daga gasar Europa bayan da hukumar UEFA ta yanke hukuncin cewa ta yi asarar wasanta da Rennes da aka dage a baya.
An dai dage wasa tsakanin Tottenham da Rennes na ranar 9 ga watan Disamba sakamakon bullar annobar corona a kungiyar ta arewacin London, bayan da gwaji ya tabbatar ‘yan wasanta 13 sun harbu da cutar.
A hukuncin da ta yanke, hukumar ta Uefa ta ce ba za a sake wasan ba, kana ta mika batun ga kwamitin da ke kula da dokokinta.
Kwamitin ya yanke hukuncin cewa an bai wa Rennes nasara 3-0, kuma ita ce ke kan gaba a rukunin nasu, Vitesse na biye, kana Tottenham ke matsayi na 3.
A wata sanarwam, Tottenham ta caccaki hukuncin na Uefa, sai dai ta ce ya zame mata dole ta karbi hakan, ta kuma mayar da hankali a sauran wasannin da suka rage mata a gasar da take ciki.
0 Comments