Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

TSARO: Ba Lallashi Muke So Ba, Gyara Muke So, Cewar Kwamared Salihi

Daga Fatima Idris Zariya A ci gaba da jin ra'ayin shuwagabanin matasa a kasa baki daya, wakiliyarmu ta zanta da Kwamared Jib...


Daga Fatima Idris Zariya

A ci gaba da jin ra'ayin shuwagabanin matasa a kasa baki daya, wakiliyarmu ta zanta da Kwamared Jibrin Salihi akan halin da kasa ke ciki a yanzu musamman a bangaren tsaro  

Idan masu karatu ba su manta ba a 'yan kwanakin nan an sami kalubalen tsaro da ta kai an sami wasu da ake tunanin 'yan bindiga ne sun tare motar haya dauke da mutane kusan 40 maza da mata da kananan yara duka suka banka masu wuta take suka yi kurmus a wannan waje.

Wannan rashin tausayin ne ya kawo cece-kuce mai zafi tsakanin al'ummar kasa baki daya musamman 'yan Arewa.

Bisa haka ne kungiyoyi matasa da yawa a fadin kasarnl nan suka dau aniyar nuna damuwarsu ta hanyar fitowa yin zanga-zangar lumana a fadin jihohin Arewa.

Ganin yadda matasan a jihar Bauchi da jihar Kano suka fito suna nuna takaicinsu ga abubuwan da suke faruwa a fadin kasa baki daya.

Bisa haka ne wakiliyarmu  ta zanta da shugaban majalisar matasa na karamar hukumar Sabon Gari ta jihar Kaduna wato Kwamared Jibril Dalihi ta wayar Salula akan wannan lamari.

Salihi sai ya ce, "Inna lillahi wa'inna Ilaihin Rajju'un".

Shugaban ya ci gaba da mika sakon ta'a'ziyyarsa ga dukkan iyalan wadanda suka rasa rayukansu a kasa baki daya.

Bayan haka shugaban ya ce duk da kokarin da gwamnati ke yi ya kamata ta kara jan damara sosai.

Tuni shugaban majalisar matasan ya kara da cewa su fa ba hakuri suke neman gwamnati ta ba su ba ya ce aiki suke so su gani a kasa.

Da yake bai wa matasa kasa shawara kuwa, cewa ya yi don Allah ka da matasa su kauce dokar kasa wajen nuna damuwarsu akan abin da yake faruwa ya ce, hakan zai taimaka wajen isar da sakon da suke son isarwa a duniya baki daya.

A karshe kuma shugaban ya yi kira ga ita hukuma da ta yi koyi da kasashen waje wajen bai wa zanga-zangar lumanar kariya domin akwai dokar da ta bayar da damar yin hakan.

Ya yi fatan gwamnati za ta kara kaimi wajen kawo tsaro fiye da yadda ta saba a kasa baki daya.

No comments