Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

TSARO: Buhari Ya Yi Iya Abin Da Zai Iya Yi, Cewar Obasanjo

Tsohon shugaban Nijeriya Olusegun Obasanjo ya sake jaddada matsayinsa na ci gaba da dorewar Nijeriya a matsayin dunkulalliyar ka...

Tsohon shugaban Nijeriya Olusegun Obasanjo ya sake jaddada matsayinsa na ci gaba da dorewar Nijeriya a matsayin dunkulalliyar kasa sabanin yadda wasu bangarori ke fafutukar ganin sun balle domin kafa kasa ta kan su.

Yayin da yake gabatar da jawabi a wajen wani taro da Cibiyar zaman lafiya ta shirya wanda ke karkashin Mai Alfarma Sarkin Musulmin Nijeriya Muhammad Sa’ad Abubakar da tsohon shugaban kungiyar Kiristoci ta kasa Cardinal John Onayekan, Obasanjo yace ya zama wajibi kowanne ‘dan Najeriya ya bada gudumawarsa wajen tunkarar matsalolin da suka addabi kasar.

Tsohon shugaban ya ce kuskure ne mutane su dinga rungume hannun su suna cewa babu ruwan su da abin da ke faruwa ko kuma suce abinda ke faruwa wata matsala ce ta wata shiya wadda bata shafe su ba.

Obasanjo ya ce a matsayin sa na ‘dan kabilar Yarbawa ba zai taba goyan bayan kafa kasar Yarbawa zalla ba, domin kuwa shi ya amince da ci gaba da zaman Nijeriya a matsayin kasa guda.

Tsohon shugaban ya ce bai taba amfani da kabilarsa wajen neman biyan bukata a Nijeriya ba, saboda shi ya amince da cewar Nijeriya ta fi karfin kowacce kabila ko addini ko kuma shiya.

Shugaban ya bayyana cewar duk matsalolin da ake samu a kasar, abu guda da ba za’a taba samun su da laifi akai ba, shine jajircewar su na ganin Nijeriya ta ci gaba da zama kasa guda.

Obasanjo ya ce shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi iya bakin kokarinsa, kuma abin yi yanzu shi ne mayar da hankali akan shugabancin da za a samu bayan shi, wanda ake saran ya dora daga inda ya tsaya.

Tsohon shugaban ya yi gargadi dangane da yara miliyan 14 da basa zuwa makaranta a wannan lokaci, inda ya bukaci daukar matakin ilmantar da su domin hana su zama wadanda boko haram za ta dauka nan da shekaru 10 masu zuwa.

No comments