Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

Tsofaffin Daliban GGUSS Malam Madori Sun Ƙaddamar Da Gidauniyar Gyaran Makarantar Da Tallafawa Dalibai Marasa Galihu

Daga Abubakar M Tahir Hadejia Tsaffin Daliban Makarantar ƴan mata ta garin Malam Madori aji na 86 sun kaddamar da gidauniyar tal...


Daga Abubakar M Tahir Hadejia

Tsaffin Daliban Makarantar ƴan mata ta garin Malam Madori aji na 86 sun kaddamar da gidauniyar tallafawa marasa karfi dake cikin dalibai tare da gudanar da ayyukan al'kairi ga makarantar.


Taron Wanda kungiyar mai Suna (MADOGSAJ) ya samu halartar darururan mata daga Jihohin Kano, Jigawa da dai sauransu wanda suka kammala makarantar.


Da farko an bude taro da addu'a sannan aka gabatar da karatun Al'qurani mai girma bayan gamawa kuma taken Nigeria ya biyo baya.


Bayan gabatar da jawabin maraba, Shugaban Kungiyar ta MADOGSAJ Hajiya Hajara Idris Dan Batta ta gabatar da taikacaccen tarihin Kungiyar Dama Irin nasarori da suka samu ciki kwa harda Gyaran Masallacin cikin hostel wanda ya lakume kudi sama da miliyan daya sannan sun gina bandakai a cikin makataranta.


Bayan Kammalawa jawabinta Turakin Hadejia Alhaji Dauda Yusuf  ya nuna farin cikinsa kan wannan kokarin na daliban inda ya bayyana Masarautar Hadejia tana farin ciki ga wannan kokari nasu.

A karshe ya kira ga sauran kungiyoyi su dage wajen tallafawa al'umma domin samarwa al'umma cigaba mai dorewa.


Shima a nasa Jawabin Magajin Rafin Hadejia Alhaji Muhammad Babandade ya bayyana irin kokarin da yayi wajen samar da wannan makaranta tun a zamanin Jihar Kano.


Babandade ya bayyana wani kokari daya aikata  na Dasa bishiyoyi a farfakiyar makaranta.

Bayan Kammala jawaban manya baki, Yan Kungiyar MADOGSAJ sun gabatar da karramawa ta musamman ga malamansu da wanda suka tallafa musu da abubuwan alkairi.


Bayan kammala karramawa an gudanar da bude asusun gidauniyar inda Manya Ƴan Siyasa,Masarauta da Masu kudi suka kaddamar da  bada tallafinsu na kudaden cigaban gidauniyar.

Bayan Kammala taron daliban sun gudanar daukan hotuna na murna da farin cikin wannan rana mai muhimmanci a garesu.

A karshe Shugaban Kungiyar ta MADOGSAJ ta gana da ƴan jarida
Inda ta bayyana dimbin godiyarta ga al'umma da suka halarta dama wanda suka bada nasu tallafin.

No comments