Tsohon Hafsan Sojan Nijeriya, Janar Mohammed Inuwa Wushishi, ya rasu. Marigayin ya rasu ne a birnin Landan, kamar yadda iyalansa suka shai...
Tsohon Hafsan Sojan Nijeriya, Janar Mohammed Inuwa Wushishi, ya rasu.
Marigayin ya rasu ne a birnin Landan, kamar yadda iyalansa suka shaida wa manema labarai.
Janar Wushishi ya yi aiki ne da gwamnatin Shehu Shagari a shekarar 1981 zuwa 1983.
An haife shi a Ƙaramar Hukumar Wushishi da ke Jihar Neja a arewacin Nijeriya a shekarar 1940.
Tsohon sojan ya riƙe muƙamai da dama a rundunar sojan Nijeriya, inda har ya kai muƙamin Laftanar Janar.
No comments