Tsohon shugaban hukumar wasannin tsalle-tsalle da guje-guje ta duniya, Lamine Diack ya rasu ya na da shekaru 88 a rayuwarsa kama...
Tsohon shugaban hukumar wasannin tsalle-tsalle da guje-guje ta duniya, Lamine Diack ya rasu ya na da shekaru 88 a rayuwarsa kamar yadda iyalansa suka tabbatar wa Kamfanin Dillancin Labarai na AFP.
Marigayin
dan asalin Senegal ya jagoranci hukumar ta IAAF tsakanin shekarar 1999 zuwa
2015 kafin daga bisani a tuhume shi da laifin cin hanci da rashawa.
Wata
kotun Faransa ce ta same shi da aikata laifi a shekarar 2020 bayan an zarge shi da karbar miliyoyin kudade
domin yin rufa-rufa game da ‘yan wasan Rasha masu kwankwadar miyagun kwayoyi.
A
wancan lokaci, an zartar masa da hukuncin zaman gidan kaso na tsawon shekaru
hudu, amma daga bisani aka soke shekaru biyu tare da cin sa tarar Dala dubu
560.
Marigayin
ya taba zama kusa a Hukumar Wasannin Olympics ta Duniya tsakanin 1999 zuwa
2013.
No comments