Turkiyya Ta Ce Za Ta Taimakawa Nijeriya Magance Matsalar Tsaro – Buhari


Shugaban kasa Muhammadu Buhari da ke ziyarar aiki a Turkiyya ya ce ƙasar ta yi alƙawarin taimakawa Nijeriya magance ƙalubalen tsaro da ke damunta.

Sanarwar da fadar shugaban na Nijeriya ta fitar ta ce shugaban Turkiyya ne ya yi tayin taimakawa Nijeriya kan fannin sha’anin tsaro.

“A ci gaba da ƙoƙarin tabbatar da zaman lafiya a Nijeriya, shugaba Muhammadu Buhari, ya ce Najeriya za ta haɗa gwiwa da Turkiyya wajen tunkarar ƙalubalen tsaro da ƙasar ke fuskanta,” in ji sanarwar.

A cewar sanarwar shugaba Buhari ya yi godiya ga shugaban Turkiyya kuma a ganawar da shugabannin biyu suka yi ya shaida masa cewa, Turkiyya ta samu ƙwarewa sosai wajen tunkarar ƙalubalen tsaro iri daban-daban kuma Nijeriya za ta amfana da ƙwarewa.

Post a Comment

0 Comments