Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

Ƙungiyar Marubutan Arewa Ta Aikawa Shugabannin Tsaron Nijeriya SaƙonHalin Da Al'ummar Arewa Ke Ciki

... Haka zalika ƙungiyar ta bukaci Gwamnatin Najeriya da ta ɗauki matakin gaggawa don kawo ƙarshen matsalolin rashin tsaron da y......Haka zalika ƙungiyar ta bukaci Gwamnatin Najeriya da ta ɗauki matakin gaggawa don kawo ƙarshen matsalolin rashin tsaron da yayi muni a yankin Arewa.

Daga Ƙungiyar "Arewa Media Writers"

Ƙungiyar marubutan Arewa "Arewa Media Writers" ƙarƙashin jagorancin shugaban ƙungiyar na ƙasa Comr Abba Sani Pantami, ta turawa shugabannin hukumomin tsaron Najeriya sakonnin halin da al'ummar Arewa suke ciki na taɓarɓarewar tsaro, musamman a ƴan kwanakin nan.

Haka zalika ƙungiyar ta buƙaci Gwamnatin ƙasar da ta tashi tsaye kan taɓarɓarewar tsaron da yayi muni a yankin Arewa dama ƙasar Najeriya baki ɗaya.

Ƙungiyar ta bayyana hakan ne, a cikin takaddun ƙorafi da ta turawa hukumomin tsaron mai ɗauke da sa hannun shugaban ƙungiyar na ƙasa Comr Abba Sani Pantami, inda ƙungiyar ta bayana irin takaici da jimamin halin da al'ummar Arewa suke ciki, na rashin zaman lafiya, rashin kwanciyar hankali, ga kuma talauci da tsadar Rayuwa da al'ummar yankin suke ciki.

Ga wani sashi na saƙon da ƙungiyar ta turawa hukumomin tsaron;

"Mun yi imanin cewa kuna da kayan aiki don kawo ƙarshen waɗannan matsalolin, amma abin takaici ba mu ga wani sakamako mai kyau ba har yau.

"Don magance waɗannan matsalolin, dole ne gwamnati ta ƙara yawan jami’an tsaro akan jami’an da muke da su, tare da samar da guraben ayyukan yi da dama ga matasanmu.

"Akwai buƙatar matasanmu su kasance masu ilmi musamman waɗanda ke zaune a yankin da babu makarantu, asibitoci, ruwa, hanyoyi da sauransu.
 
"A ƙarshe, muna buƙatar ɗaukar matakin gaggawa don kawo ƙarshen matsalolin. 

"Muna son zaman lafiya da adalci wanda zai iya haifar da ingantacciyar rayuwa ta al’ummarmu a dukkan jihohin Arewa da Najeriya baki ɗaya.  

"Arewa Media Writers" za ta ci gaba da ƙoƙarin kawar da duk wasu labaran ƙarya da ka iya kawo matsala a wurin yaƙi da ƴan ta'addan tare da cigaba da wayarwa al'umma kai domin samun ci gaba da haɗin kai da cikakken haɗin kan Al'ummar mu. Mungode da fahimtar sakonmu.

Saƙonnin ƙungiyar ya isa ga hukumomin tsaron ƙasar, kamar yadda zakuga saka hannun tambarin hukumomin tsaron amsar saƙo a jikin takaddun shaidar isar da saƙonnin, "acknowledgement".


Ga jerin hukumomin da ƙungiyar ta isar da saƙonnin;


1, Shugaban rundunar sojin ƙasa na Najeriya.

The Chief of Army Staff,
Lt. General Faruk Yahaya.


2, Shugaban rundunar sojin sama na Najeriya.

The Chief of Air Force,
Isiaka Oladayo Amao.


3, Shugaban rundunar ƴan sandan Najeriya.

The Inspector General of Police, 
Usman Alkali Baba.


4, Shugaban hukumar jami'an tsaro na farin kaya.

The Department of State Services (DSS),
Yusuf Bichi Magaji.


Ƙungiyar "Arewa Media Writers" ta zuba ido don ganin irin matakin da hukumomin tsaron ƙasar zasu ɗauka na kawo ƙarshen matsalar rashin tsaron da ya addabi yankin Arewa dama ƙasar Najeriya baki ɗaya.

No comments