Wani Uba Ya Maka Ɗansa Kotu Yana Neman Wani Kaso Na AlbashinsaWani uba a Kenya ya kai ƙarar ɗansa yana neman kashi 20 na albashin ɗan ya shiga aljihunsa

Gideon Kisira Cherowo, mai shekara 73, ya ce ya sayar da filinsa da duk ƙadarorinsa domin yin ɗawainiya da karantun ɗansa har zuwa matakin jami’a.

Ya ce ɗansa wanda yanzu shekarunsa 48 ba ya taimakonsa.

Mahaifin wanda ke da ƴaƴa huɗu ya ce ɗaya daga cikinsu ne kawai ke aiki a hukumar sufurin jiragen sama ta Kenya.

Mista Cherowo na zama ne da iyalinsa a gidan ƙasa a wani ƙauye da ke yammacin Kenya.

Jaridar Daily Nation ta wallafa hoton mutumin a Twitter.

Ya yi zargin cewa ɗansa ya shafe shekara 17 bai ziyarci gida ba kuma shi da iyalinsa sun nemi taimakonsa. 

(BBC)

Post a Comment

0 Comments