Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Yadda Ƴan bindiga Suka Kona Wata Motar Fasinja Dauke Da Mutum 42 A Sakkwato

A yayin jana'izar mutanen da 'yan bindigar suka kona.  Rahotanni daga jihar Sakkwato da ke arewacin Nijeriya na cewa ‘ya...

A yayin jana'izar mutanen da 'yan bindigar suka kona. 

Rahotanni daga jihar Sakkwato da ke arewacin Nijeriya na cewa ‘yan bindiga sun kona wata motar fasinja dauke da mutum 42.

Rahotannin sun ce fasinjojin sun fito ne daga karamar hukumar Sabon Birni da ke jihar domin yin ƙaura zuwa wasu yankunan Nijeriya, saboda ta'azzarar ayyukan 'yan bindiga a inda suke.

Wasu shaidu sun cewa BBC lamarin ya faru ne da misalin karfe 9 na safiyar ranar Litinin.

"Motar ɗauke da fasinjojin ta tashi daga Sabon Birni, ta yi tafiyar da bai fi kilomita shida ba zuwa kauyen Gidan Bawa inda wannan masifa ta afka mata," kamar yadda wadanda suka yi aikin ceton suka bayyana wa BBC.

Tuni dai aka yi jana'ziar mamata in ji shaidu.


BBC ta yi ƙoƙarin jin ta bakin rundunar ƴan sandan jihar, amma haƙarmu ba ta ci cimma ruwa ba, ko da muka kira kakakin, wayarsa a kashe take.

Kazalika mun kira kwamishinan tsaro na jihar har sau uku shi ma bai ɗauka ba.

Wani ganau ya cewa BBC: "Lokacin da abin ya faru ina Sabon Birni aka kira ni aka shaida min. Daga cikin matafiyan ma har da wani ƙanin mahaifiyata da matarsa da ƴaƴansu huɗu.

"Cikin ƴaƴan Allah Ya yi wa biyu rasuwa. Lokacin da muka isa wajen da ya faru mun je mun iske mutane sun mutu, kuma a ƙalla mun ƙirga gawarwaki sun kai 25," ya ce.

Ya ƙara da cewa akwai tsirarun mutane daga cikinsu da suka tsira.

Shi ma wani shaidan da ya buƙaci a sakaya sunansa ya ce "mutum 45 ne a cikin motar, amma bakwai ne suka tsira da rayukansu, su ma a yanzu haka suna cikin halin ha'ula'i.

"Babu maganar ma ka ga gawa a kammale, sai dai muka dinga haɗa ƙafafu da hannaye daban-daban aka yi musu jana'iza a tare."


Ya ce shi yana tsaye a tasha ma lokacin da motar ta tashi. "Ƴan Union ne ma na tasha suka gaya mana adadin mutanen da motar ta tashi da su," a cewarsa.

Yankin arewa maso yammacin Nijeriya na ɗaya daga cikin yankunan da suka fi fama da matsalar tsaro a Nijeriya, sai dai a lokuta da dama gwamnatocin yankin na cewa suna iya kokarinsu domin tabbatar da kare rayuka da dukiyoyin al'umarsu, abin da al'umar ke cewa ba sa gani a kasa.


No comments